Jahar Kano Za Ta Hada Gwiwa Da Canada A Fannonin Bunkasa Lafiya, Ilimi, Noma.
Gwamnatin jihar Kano ta sake bayyana kudurinta na hada gwiwa da kasar Canada a fannonin kiwon lafiya, ilimi, noma, da sauran fannonin ayyukan dan adam domin amfanin bangarorin biyu. Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin jakadan kasar Canada a Najeriya, mai girma James Christoff wanda ya kai masa ziyara a ofishinsa da ke gidan gwamnatin Kano a yau. Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi tsokaci kan kyakkyawar alakar da ke tsakanin Kano da gwamnatin Canada a fannonin ilimi, noma, kimiyya da fasaha da dai sauransu. A cikin wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, mai magana da yawun gwamnan ya ce, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na da manufar samun moriyar juna, kuma Kano za ta ci gaba da samar da duk wani yanayi da ya dace domin hadin gwiwar yin aiki. Gwamnan ya kuma nemi taimako a fannonin sauyin yanayi, ban ruwa na zamani da sake farfado da shirin bayar da tallafin karatu ga ‘yan asalin Kano da aka yi a farkon shekarun 80s. ...