Nan Ba Da Jimawa Ba Matsalar Ruwa Za Ta Zama Tarihi A Kano - Kwamishina
Gwamnatin jihar Kano ta ce tana bakin kokarinta wajen ganin ta shawo kan matsalar karancin ruwan sha a birnin Kano da kewaye. Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Dr Ali Haruna Makoda ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Kano ranar Laraba. “Muna aiki tukuru domin ganin mun gyara matsalar karancin ruwan sha a babban birnin jihar da kewaye, kuma nan ba da jimawa ba za a kawo karshen matsalar,” inji Makoda. Ya dora alhakin kalubalen a kan cikakken kayan aiki, musamman a cibiyar kula da ruwa ta Tamburawa da ke samar da ruwa ga mafi yawan sassan birnin Kano. Ya ce tsananin zafin da ake fuskanta a yankin shi ma ya jawo matsalar karancin ruwan, yayin da mutane ke amfani da ruwa mai yawa don jure yanayin. A cewarsa, gwamnatin jihar ta gaji lalacewar sha’anin ruwa daga gwamnatin da ta shude wanda ba ta ba da kulawar da ya kamata ba wajen samar da ruwan sha. A lokacin gwamnatin da ta shude, kwamishinan ya ce kashi 20 cikin 100 na bukatun ruwan jihar ne kawai ake samar ...