Posts

Showing posts with the label Kwallon kafa

Barcelona Ta Lashe La Liga Karon Farko A Shekaru Hudu

Image
Barcelona ta lashe gasar La Liga a karon farko cikin shekaru hudu, bayan samun nasarar lallasa Espanyol da ci 4-2 a wasan da suka fafata a ranar Lahadi. Robert Lewandowski ne ya ci wa Barcelona kwallaye biyu sai kuma na farko tun bayan zuwansu Barca da Alejandro Balde da Jules Kounde suka jefa wa kungiyar. A yanzu Barcelona ta bai wa Real Madrid tazarar maki 14 da ke biye da ita a mataki na biyu yayin da ya rage wasanni hudu a karkare La Liga ta bana. Barca ce kungiyar da babu kamarta a fagen tamaula a Sifaniya a bana, inda ta rika jan ragama a saman teburin La Liga tun daga wasan mako na 13. Barcelona ta lashe La Liga jimilla 27 a tarihi, kuma wannan ita ce ta kakar wasa ta farko da tsohon dan wasan kungiyar, Xavi Hernandez ya jagorance ta a matsayin koci. Sai dai duk da wannan bajinta da Barcelona ta yi a iya La Liga, ta gaza kai bantenta a nahiyar Turai, inda aka tankado keyarta tun daga zagayen rukuni a Gasar Zakarun Turai, sannan kuma bayan ta koma Gasar Europa, a can

Messi da Mbappe da Neymar sun yi wasa tare karon farko bayan kofin duniya

Image
A ranar Lahadi Kylian Mbappe da Lionel Messi da kuma Neymar suka buga wa Paris St Germain wasa tare karon farko tun bayan kammala Gasar Kofin Duniya a Qatar. Argentina ce ta lashe kofin da Messi ya daga, bayan da suka yi nasara a kan Faransa tawagar Mbappe, yayin da Brazil ta Neymar ba ta kai bante ba. Sun kuma buga wasan Ligue 1 na faransa fafatawar zagaye na 19, inda Rennes ta yi nasara da ci 1-0. Tun farko an bai wa Messi karin lokacin hutu, domin ya samu damar murnar lashe kofi da suka yi wa kasar na uku jumulla Sai dai kuma Messi ya ci kwallo da ya koma yiwa PSG tamaula a tsakiyar mako da ta tashi 2-2 da Angers. Shi kuwa Mbappe bai samu buga wasa biyu ba, bayan da ya je hutu birnin New York tare da abokinsa Achraf Hakimi. An sa ran za a fara wasa da Mbappe ranar ta Lahadi, sai ya fara da zaman benci daga baya ya canji Hugo Ekitike, inda ya hadu da Messi da Neymar daga gaba.

Al Nassr za ta mutunta hukuncin dakatarwar wasanni 2 kan Ronaldo

Image
  Kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr a Saudi Arabia ta tabbatar da shirin mutunta hukuncin hukumar kwallon kafar Ingila kan sabon dan wasan da kungiyar ta saya Cristiano Ronaldo game da haramcin wasanni biyu da ke kansa Wani jigo a Al Nassr ya shaidawa AFP yau juma’a cewa tauraron na Portugal mai shekaru 38 ba zai taka leda a wasanni biyu da kungiyar za ta doka nan gaba ba, domin mutunta hukuncin.   Tun a watan Nuwamba ne dai, hukumar FA ta dakatar da Ronaldo a wasanni biyu saboda samunsa da laifin jifan wani magoyin bayan Everton da wayar salula lokacin da ya ke shirin daukar hotonsa bayan rashin nasarar Manchester United hannun Everton a Goodison Park. Har zuwa yanzu dai Al Nassr ba ta yiwa Ronaldo rijista ba, kasancewar kungiyar ta zarta adadin ‘yan wasa 8 sa hukumar kwallon kafar Saudiya ta sahale mata saye daga ketare duk kaka. Zuwa yanzu dai Al Nassr ta sayi ‘yan wasan da yawansu ya kai 9 daga ketare ciki har da Ronaldo da ta sayo kan yuro miliyan 200 bayan dan wasan gaban na Port

Kungiyoyi da dama sun so daukata amma na yi wa Al-Nassr alkawari - Ronaldo

Image
Cristiano Ronaldo ya ce kungiyoyin kwallon kafa da dama a sassan duniya sun nuna sha’awar daukar sa amma ya yanke shawarar sanya wa Al-Nassr hannu. A lokacin da Al-Nassr ta gabatar da shi a matsayin dan wasanta a gaban dubban magoya bayan kungiyar a ranar Talata, Ronaldo ya bayyana cewa kungiyoyi a nahiyar Turai da Brazil Amurka da Australia da Portugal sun nemi su dauke shi amma ya zabi zuwa Saudiyya. Jaridar Aminiya ta rawaito Ronaldo na cewa “Kamar yadda na fada a baya wannan dama ce a gare ni ba wai a harkar kwallon kafa ba, dama ce da zan sauya tunanin matasa masu tasowa. “Kungiyoyi da dama daga Nahiyar Turai da Brazil da Amurka da Australia da ma Portugal son so dauka ta amma na yi wannan kungiya alkawari. “Na san abin da nake so da wanda ba na so, kuma wannan babban kalubale ne a gare ni na zuwa wannan kasa, ba don komai ba sai don na kara samun ilimi. “Ina son sabon yanayi, kasa don cimma wani buri na daban tare sa Al-Nassr, wannan shi ne dalilin da ya sa na rungumi

Fitaccen dan kwallon duniya, Pele ya mutu

Image
  Fitaccen É—an Æ™wallon nan na duniya É—an Æ™sar Brazil, Pele ya rasu yana da shekara 82. Pele ya rasu ne a ranar Alhamis 29 ga watan Disamban 2022 bayan ya sha fama da rashin lafiya. A kwanakin baya an yi ta yaÉ—a labarin Æ™arya na rasuwarsa. Ya rasu ne sakamakon cutar kansar Æ™aba da kuma cutar Æ™oda Ana ganin Pele shi ne É—an Æ™wallon da ba a taÉ“a samun irin sa ba a duniya, kuma sau uku yana cin gasar kofin duniya wa Æ™asarsa Brazil. Ya ci kofin duniya a shekarun 1958 da 1962 da kuma 1970. A shekarar 2000 ne kuma hukumar Æ™wallon Æ™afar duniya FIFA, ta ayyana shi a matsayin É—an Æ™wallon Æ™arni. Shi ne É—an Æ™wallon da ya kafa tarihin zura Æ™wallaye 1,281 a raga a cikin wasanni 1,363 cikin shekara 21 da ya yi yana buga tamaula. Cikin waÉ—annan har da Æ™wallo 77 da ya ci wa Æ™asarsa cikin wasanni 92 da ya buga wa Brazil É—in. An yi wa Pele tiyata a kan yanke masa kansa a hanjinsa a watan Satumban 2021 a Asibitin Albert Einstein da ke Sao Paulo. An sake kwantar da shi a asibiti a watan Nuwamban 2022. Ƴarsa