Posts

Showing posts with the label Jita-Jita

Jita-Jitar Satar Naira Biliyan 50 a NAHCON: Babu Shaida, Babu Gaskiya - Ganiyu Lamidi

Image
Daga Ganiyu Lamidi A Najeriya, jita-jita kan zama kamar gaskiya idan aka yi ta maimaitawa. Labaran karya kan shafe na gaskiya, saboda mutane suna son jin labaran Al'ajabi, shakku ko mamaki. Mun taba jin labarin Madam Koi-Koi da Iliya dan Mai-Karfi, duk da ba gaskiya ba ne, amma mutane sun dade suna yada wannan labaran. Yanzu haka, Hukumar Alhazan Najeriya, NAHCON, da Shugabanta Farfesa Abdullahi Saleh Usman, sun fada cikin irin wannan jita-jitar. Zargin wai an sace Naira biliyan 50 a hajjin da ya gabata. Labarin ya yadu Kamar wutar daji a kafafen sada zumunta da jaridu, amma babu wata hujja ko gaskiya cikin lamarin. Zargi ne kawai da 'Yan siyasa ke kara rura wutarsa. Idan muka duba lamarin a hankali, za mu ga cewa wannan magana bata da tushe. A 2025, alhazai daga kudanci sun biya kusan Naira miliyan 8.78, yayin da na arewa suka biya Naira miliyan 8.46. Idan aka raba Naira biliyan 50 da wannan farashi, zai bamu adadin alhazai kusan 5,700. Wato sai mutum ya karbi kudi...