Abin Da Ya Kawo Cikas A Sulhun ECOWAS Da Sojin Nijar — Yusuf Tuggar
Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce sun yi tayin tattaunawa domin kawo ƙarshen tankiyar da ke tsakanin Ƙungiyar Raya Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) da sojojin da suka kifar da Shugaban Nijar Mohammed Bazoum, amma hakan bai yiwu ba, don kuwa shugabannin sojojin sun ƙi amincewa da yunƙurin. Ambasada Tuggar ya faɗi hakan ne a wata hirarsa da BBC, yana mai cewa duk wata magana da ta shafi a saki Shugaba Bazoum, sojin ba su amince da ita ba. ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 2 a Imo Abdul Amart ya siya wa iyalan Aminu S. Bono gida “Sun ce kar ma a yi wannan maganar, kar ma a sa shi cikin sharuɗɗan yin sulhu,” in ji Yusuf Tuggar. Ya bayyana cewa babu ta yadda za a iya samun sulhu a wannan yanayi. “Za su ci gaba da rike shi kenan ya yi zaman dindindin a kulle?” Ministan ya ce sojojin da suka yi juyin mulki ne suka janyo wa Nijar takunkumin da ECOWAS ta ƙaƙaba mata, da kuma shiga halin da take ciki. Ya ce abin da suke buƙata shi ne a saki Shugaba Bazou