Posts

Showing posts with the label Abba Gida-gida

Gabanin Rantsuwa: Zababben Gwamnan Kano, Abba Gida Gida Ya Bayyana Kadarorinsa

Image
Gabanin kaddamar da taron a ranar Litinin, zababben gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, (wanda aka fi sani da Abba Gida Gida) ya bayyana kaddarorin sa da kuma bashin da ake bin sa a cikin fom din da ya cike  ya mika a ranar Juma’a ga ofishin hukumar da'ar ma'aikata dake Kano  SOLACEBASE  ta rahoto cewa  Abba wanda ya samu tarba daga Daraktar hukumar ta jihar Kano Hajia Hadiza Larai Ibrahim, ya bayyana cewa kwazonsa na bayyana kadarorinsa nuni ne na gaskiya da rikon amana da zai zama ginshikin gwamnati mai zuwa a jihar Kano. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sunusi Bature Dawakin Tofa babban sakataren yada labarai na zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya fitar a ranar Juma’a. Ya ce: "A yau, na cika hakkin da kundin tsarin mulki ya dora min na bayyana kadarorina kafin na shiga Ofis, ranar 29 ga Mayu." ''Zababben Gwamna,  ya shaida wa mata cewa aikin gwamnati kira ne; hidima ce ga bil’adama kuma a shirye nake a koyaushe in ...

Yanzu-Yanzu: Nasiru Gawuna Ya Taya Abba Gida-gida Murnar Lashe zaɓen Gwamnan Kano

Image
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Kuma wanda ya yiwa jam’iyyar APC takarar gwamnan jihar kano a jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya ce ya karÉ“i Kaddarar faÉ—uwa zaÉ“e tare da taya Abba Kabiru Yusuf Murnar lashe zaÉ“en gwamnan Kano. Nasiru Gawuna ya bayyana hakan ne cikin wani sakon murya da yayi bayani na tsawon mintuna biyu, wanda Sakataren yada labaran sa Hassan Musa Fagge ya aikowa kadaura24. ” Mun tsammaci Hukumar Zabe INEC zata duba koken da mukai mata na samun kura-kurai a sakamakon zaben da ya gudana, amma a yau 29 ga watan maris ta sake tabbatar da matsayar ta ta hanyar mikawa Abba Kabiru Yusuf Shaidar lashe zabe , don haka mun dauki wannan a matsayin kaddara”. Inji Gawuna   Yace dama ya fada a baya cewa zai karÉ“i Kaddara idan ya fadi zaben don haka yayi kira ga magoya bayan sa da dukkanin al’ummar jihar kano da zu baiwa sabon zaÉ“aÉ“É“en gwamnan hadin kai don ya gudanar da mulkin sa cikin kwanciyar hankali da lumana.   Mataimakin Gwamnan ya kuma yi addu’ar Alla...