Posts

Showing posts with the label Matasa

Gwamnatin Kano Za Ta Samar Da Rumbun Tara Bayanai Na Matasa - Ogan Boye

Image
Shirye-shiryen gwamnatin Jihar Kano tare da kulawar Ofishin Mai ba wa Gwamna Shawara akan harkokin Matasa da Wasanni sun kammala wajen kirkiro da rumbun tara bayanai na Matasan Jihar Kano. Mai ba wa Gwamna Shawara akan harkokin Matasa da Wasanni Ambasada Yusuf Imam Ogan Boye ne ya shaida hakan lokacin da yake yi wa manema labaru jawabi dangane da manufa da amfanin yin rumbun tara bayanan matasan a Ofishinsa. A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na ofishin mai bawa gwaman shawara, Yusuf Ibrahim ya sanyawa hannu, Ogan Boye ya bayyana muhimmancin tara bayanan wajen taimakawa gwamnati don inganta tsare-tsaren bunkasa harkokin matasa a Jihar Kano, ya yi dogon bayani kan muhimmancin matasa a fanin kasuwanci da tattalin arzikin kasa. Yace " Ina da yakinin cewa wannan batun rumbun tara bayanan matasa zai karfafi tsare-tsaren gwamnati na samar da guraben aiyuka da sana'o'i tare da rage yiwuwar fadawar matasa miyagun aiyuka" in ji Ogan Boye. Ambasada Yusuf Imam ya ...