Kwastam ta kama tirelar shinkafa ‘yar-waje takwas da aka shigar Nijeriya
Hukumar fasa-Æ™wauri ta Nijeriya, Kwastam ta ce ta kama tirela takwas maÆ™are da shinkafa Æ´ar-waje a kan iyakokin Æ™asar da ke yankin Kudu maso Yamma. A wani taron manema labarai da Shugaban Kwastam na riÆ™o Bashir Adewale Adeniyi ya yi a Legas wanda ya ce mai matuÆ™ar muhimmanci ne ga tattalin arzikin Æ™asar, ya ce jami’an hukumar sun kama shinkafar buhu 7,029 ne a lokuta da wurare daban-daban a shiyyar Kudu maso Yammacin. Mr Adeniyi ya ce an samu wannan nasara ce bayan Æ™addamar da wasu jerin ayyuka da hukumar ta yi don ceto fannin noma na Æ™asar da ya zama babban makamin da gwamnatin tarayya ke riÆ™e da shi don inganta samar da abinci. “Kamar yadda aka sani fannin noma, wanda shi ne Æ™ashin bayan tattali arzikin Nijeriya, ya zama muhimmin abun da gwamnatin tarayya ta mayar da hankali a kai don samar da isasshen abinci ga Æ´an Æ™asar da kuma inganta tattalin arziki. “Ana gudanar da wannan samame da jami’anmu ke yi ne don abu biyu ne; karya gwiwar Æ´an kasuwar da ke son su dinga hada-h...