Kotu Ta Sauya Hukunci Kan Dakatar Da Ganduje A Matsayin Shugaban APC Na Kasa
Babbar kotun jihar Kano mai lamba hudu karkashin mai shari’a Usman Na’abba, wadda tun da farko ta yi umarnin dakatar da Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa, ta yi watsi da wannan umurnin na korar dakatar da shi A wani umarni na baya-bayan nan da kotun ta bayar kan tsohon gwamnan jihar Kano, wanda yanzu shi ne shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, an haramtawa tsohon gwamnan jihar Kano gabatar da kansa a matsayin Shugaban jam'iyyar na kasa bayan wani Haladu Gwanjo da Laminu Sani Barguma da ke ikirarin cewa shi ne shugaba da sakataren jam’iyyar na APC a mazabar Ganduje a karamar hukumar Dawakin Tofa ta jihar, suka bayar da umarnin dakatar da Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar. Sai dai kuma a wani yanayi na daban, alkalin babbar kotun jihar, Mai shari’a Usman Na’Abba, ya ce, a lokacin da ya yi watsi da umarnin da ya bayar a baya, ya ce da ya karanta takardar daukaka kara tare da takardar goyon bayan sakin layi na 27 da kuma rubutaccen ...