Posts

Showing posts with the label Gwamnan Nassarawa

Kotun Koli Ta Jingine Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Nasarawa

Image
Kotun Koli da ke zamanta a Abuja ta jingine yanke hukuncin kan shari’ar Zaben Gwamnan Jihar Nasarawa, zuwa wata rana da za ta sanar nan gaba. A zamanta na yau Talata, Kotun Kolin ta saurari muhawarori daga lauyoyin bangarorin PDP da APC, kan takaddamar kujerar gwamnan jihar, tsakanin gwamna mai ci, Abdullahi Sule na jami’iyar APC da David Emmanuel Ombugadu na jami’iyar PDP. Tun farko dai, David Emmanuel Ombugadu na jam’iyyar PDP ya garzaya gaban Kotun Kolin bayan Kotun Daukaka Kara ta ayyana Abdullahi Sule a matsayin wanda ya lashe zaben. Wannan na dai na zuwa ne saÉ“anin hukuncin da Kotun Sauraron Kararrakin zabe ta yanke inda ta ayyana David Emmanuel Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar. Aminiya ta ruwaito cewa, a watan Nuwambar bara ne Kotun Daukaka Karar ta bayyana cewa kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar ta yi kuskure wajen soke nasarar Abdullahi Sule na APC a zaben Gwamnan Nasarawa da aka gudanar ranar 18 ga Maris, 2023. Ana iya tuna cewa, ...