Posts

Showing posts with the label Ministan Aikin Hajji da Umrah

Duk kasar Da Ta Fara Shirin Aikin Hajjin 2024 Da Wuri, Za Ta Samu Zabin Wuraren Zama A Mashã'ir Ministan Hajji da Umrah Na Saudiyya

Image
Daga: Muhammad Ahmad Musa A wajen bikin kawo karshen aikin Hajjin shekarar 2023, a ranar Juma'a, Ministan Hajji da Umrah na kasar Saudiyya, Dakta Tawfiq Al Rabiah ya bayyana cewa, tawagar aikin Hajji ta farko da ta kammala dukkan shirye-shirye za ta samu damar zabar wuraren da ta fi so a masha'ir yayin aikin Hajji 2024.  Ya bayyana hakan ne a hedikwatar ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya da ke Makkah a wani taron da ya samu halartar shuwagabanni da wakilan alhazai a masarautar.   A yayin jawabin nasa, Ministan ya gode wa dukkan hukumomi da masu aikin Hajji bisa rawar da suka taka a wannan shiri na shekarar 2023 tare da jaddada aniyar Masarautar na hidimar bakon Allah a mafi kyawu ta hanyar samun ra’ayi daga ayyukan Hajji da inganta ayyukanta. Don haka ya kaddamar da taswirar aikin Hajjin 2024 da za a fara nan take tare da mika wa kowace kasa takarda da ta sanar da fara shirye-shirye da kuma tabbatar da wuraren da za ta yi aikin Hajjin 2024. Wasu daga cikin fitat...