Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, Shi Ne Ministan Da Ya fi Kowanne Nuna Kwazo A Najeriya - Triangle News Media
A ranar 6 ga Mayu, 2023, a birnin Landan na kasar Birtaniya, Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, Farfesa Isa Ali Ibrahim (Pantami) FCIIS, FBCS, FNCS, ya samu lambar yabo ta "Fitaccen Minista" ta Mujallar Triangle. A sanarwar da mataimaki na musamman ga Ministan kan kafafen sadarwa na zamani, Yusuf Abubakar ya wallafa, an bayar da wannan lambar yabon ne saboda kwazo, aiki tukuru, kyakkyawan jagoranci da kuma kwazon aiki da Farfesa Pantami ya nuna, wanda ke neman sanya bangaren tattalin arzikin na Najeriya a kan turbar ci gaba. A karkashin jagorancin Farfesa Pantami, fannin tattalin arziki na dijital ya sami nasarorin da ba a taɓa gani ba a fannonin shiga yanar gizo, fasahar dijital da kasuwanci, haɗa dijital, ka'idojin ci gaba, kariyar bayanai da sirri, da ƙwarewar dijital, da sauransu. Minista Pantami da kan sa ya jajirce wajen samar da wasu muhimman kudirori guda biyu na bangaren tattalin arzikin Najeriya, wato Nigeria Startup Act 2022, dokar da...