Labari da dumiduminsa : 'Yan bindiga sun sake yin garkuwa da fasinjojin Jirgin kasa

Watanni bayan da ‘yan ta’addan suka kai hari tare da yin garkuwa da fasinjoji da dama a cikin jirgin kasa zuwa Kaduna, wasu ‘yan bindiga sun kuma kai farmaki tashar jirgin kasa tare da kwashe mutane da yawa a Jihar Edo dake kudu maso kudancin Najeriya.

Fasinjojin da suka samu raunuka, an ce suna jiran su hau jirgin kasa a wurin da lamarin ya faru, kafin su nufi garin Warri mai arzikin man fetur.

Tuni dai hukumar 'yan sanda ta Rahotanni sun tabbatar da faruwar lamarin a cewar tashar talabijin ta TVC.

Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta ce ‘yan bindigar da ke dauke da bindigogi kirar AK-47 sun kai farmaki tashar jirgin da misalin karfe 4 na yammacin ranar Asabar 7 ga watan Janairu, inda suka yi ta harbe-harbe kafin su fito da shirinsu. 

A ranar 28 ga Maris, 2022 ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan jirgin kasa da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, inda suka kashe wasu tare da yin awon gaba da wasu fasinjoji. 2022 .

Har yanzu dai Hukumar Jiragen kasa ta Najeriya ba ta ce uffan ba game da sabon ci gaban da aka samu a daidai lokacin da ake hada wannan rahoto.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki