Maharan Jirgin Edo Na Neman Fansar N520m
’ Yan bindigar da suka sace fasinjoji a Tashar Jirgin kasa ta Ekehen da ke Jihar Edo na neman Naira miliyan 520 a matsayin kudin fansa. Rahotanni sun ce maharan sun kira iyalan fasinjoji 26 da ke hannunsu, suka yanka musu fansar Naira miliyan 20 a kan duk mutum daya. Zan dora daga inda El-Rufai ya tsaya a Kaduna —Uba Sani Kano 2023: Dalilin ba wa Gawuna takarar Gwamna —Ganduje Wani shugaban matasa a yankin, Benson Ordia, da ya tabbatar da hakan, ya ce gwamnatin jihar ta ce za ta gudanar da bincike na tsanaki a yankin. Sai dai kakakin ’yan sandan jihar, Chidi Nwanbuzor, ya ce ba shi da masaniya kan kudin fansar da maharan suka yanke kan fasinjojin. A ranar Asabar ce maharan suka kai hari tare da yin awon gaba da fasinjoji akalla 32 a tashar jirgin kasan. Sai dai jami’an tsaro sun ceto mutum shida daga cikin fasinjojin jirgin kasan da aka sace, wadanda uku daga cikinsu kananan yara ne. Wannan dai shi ne karo na biyu da ’yan bindiga ke kai wa jirgin kasa hari tare da sace fasi...