Posts

Showing posts with the label Sabuwar Gwamnati

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sake Sanar Da Nadin Sabbin Mukamai A Gwamnanatina

Image
Gwamnan Jihar Kano Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da karin mukamai biyar a mukamai daban-daban. A cewar sanarwar da babban sakataren yada labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, ta ce wadanda aka nada sune kamar haka. 1. Injiniya Garba Ahmed Bichi Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano 2. Dr. Rahila Mukhtar Babban Sakataren Hukumar Kula da Gudunmawar Kiwon Lafiya ta Jihar Kano (KCHMA). 3. Hassan Baba Danbaffa Manajan Darakta na Hukumar Kula da Tituna ta Jihar Kano (KARMA). 4. Arc. Ibrahim Yakubu Manajan Daraktan hukumar tsara Birane ta Jihar Kano (KNUPDA). 5. Abdulkadir Abdussalam Akanta Janar na Jihar Kano Nan ba da jimawa ba za a sanar da bikin rantsar da wadanda aka nada domin ba su damar sauke nauyin da aka dora musu nan take.