Hukumar DSS ta kama tsohon Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaben dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP, Doyin Okupe
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama tsohon Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaben dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP, Doyin Okupe. A cewar Tolu Babaleye, lauyan Okupe, an kama dan siyasar ne a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Ikeja a Jihar Legas, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Landan. Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, ta samu Okupe, mai bai wa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan shawara kan Harkokin Jama’a, da laifin karkatar da kudaden makamai daga Ofishin mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro. Mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta bayyana cewa, masu tuhuma sun gabatar da karar satar kudi a kan Okupe wanda aka ci shi tarar Naira miliyan 13. Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, A shekarar 2019, Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziki Zangon Kasa, ta tuhumi Okupe da laifuka 59 ciki har da wadanda suka shafi karkatar da kudi har Naira miliyan 240 daga hannun Sambo Dasuki. An gurfanar tare da shi tare da wasu kamfanoni biyu – Value T