Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Yi Kira Ga Masu Gidajen Man Fetur Dasu Dasu Siyar Da Mai A Tsohon Farashi
Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusif ya bukaci ‘yan kasuwar man fetur da su dawo da farashin man fetur na baya domin rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta a halin yanzu. A sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, tace Gwamnan ya ce yana sane da cewa har yanzu ‘yan kasuwar na da tsohon man fetur da ya kamata a sayar da shi a tsohon farashi. Domin rage wahalhalun da ‘yan jihar ke fama da su, ya kamata ‘yan kasuwa su yi hakuri su sake bude duk gidajen mai da kayayyakin da ake da su a hannun jari don sayarwa a kan tsohon farashi. “A matsayina na Gwamna, na ji takaicin ganin yadda Al’ummarmu na Kano ke shan wahala sakamakon hawan man fetur da bai dace ba, kuma dole ne a kawo karshen lamarin nan take.” Inji Gwamnan. Kano a cewar Gwamna Abba Kabir, ita ce cibiyar kasuwanci a yankin arewacin kasar da kuma wasu kasashe a yammacin Afirka, kuma al'ummarta masu tarin yawa na ci gaba da samun kyakkyawan yanayin kasuwanci.