An Kama Mai Gyaran Wuta A Cikin Likitocin Bogi Masu Aiki A Asibitoci Fiye Da 100 A Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta cafke wani mai gyaran wutar lantarki a cikin jerin likitocin bogi masu aiki a fiye da asibitoci da wuraren karbar magani 100 a jihar.
Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa, a duk cikin likitocin na bogi, guda daya ne kacal ya mallaki kwalin sakandire kamar yadda bayanan kwamitin masu bincike suka nuna.
Haka kuma, an samu wani mai gyaran wutar lantarki a cikin jerin likitocin na bogi da yake duba marasa lafiya a wani asibiti mai gado takwas.
An gano wannan asibiti ne dai tare da karin wasu 129 yayin binciken kwamitin da Shugaban Karamar Hukumar Tudun Wada, Ahmad Tijjani Matata ya kaddamar.
Karafe ya ce daya daga cikin likitocin bogin ya tsiyaya wa wata mata jini mai dauke da kwayoyin cutar HIV a jikinta, duk da kuwa cutar zazzabin cizon sauro kadai ta yi korafin tana fama da ita.
“Wannan abin takaici ya kai intaha, domin kuwa mun samu wani mai gyaran wutar lantarki a daya daga cikin asibitocin yana duba marasa lafiya har da karin jini da ruwa da rubuta magani da kuma duba mata masu juna biyu.“Akwai daya daga cikin likitocin bogin da ya kara wa wata mata jini mai dauke da kwayoyin cutar HIV.
“A yanzu duk mun mayar da marasa lafiyar asibiti domin samun kulawar da ta dace, kuma galibi ba su da wata masaniya a kan abin da ya shafi kiwon lafiya.
“Wani daga cikinsu ma cewa ya yi shi malamin kula da masu jinya ne, amma da muka yi bincike mun gano kwalin sakandire kadai ya malla
ka,” a cewar Karafe.