MAI MARTABA SARKIN KANO ALHAJI AMINU ADO BAYERO: Baƙon Shehu Maghili
Daga: Magaji Galadima A ranar Litinin 12 ga watan Disamba 2022 gwamnatin ƙasar Aljeriya ta aiko da wani jirgi na musamman domin ya ɗauki mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zuwa ƙasar ta Aljeriya domin halartar taron duniya na musamman don tunawa da rayuwa da kuma aiyukan shahararren malamin addinin Musulunci sharifi kuma masanin falsafa wato Shehun malami Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na goma sha biyar. Jigin ya tashi daga Kano da karfe 9:45 na safe. A cikin waɗanda suka samu alfarmar raka Sarki wannan tafiya akwai Sarkin Dawakin Tsakar-gidan Kano Alhaji Ahmad Ado Bayero hakimin Kumbotso da Ambasada Ahmad Umar Ɗanmalikin Kano da Dakta Ibrahim Ɗahiru Bauchi wanda ya wakilci Sheikh Ɗahiru Bauchi da Malam Isa Sanusi Bayero da Dakta Lawi Atiku Sanka da kuma ni Magaji Galadima Kachallan Kano, sannan sai wasu malamai da sharifai na Kano da kuma fadawa hadiman Sarki. Jirgin ya ɗan yada zango a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nija...