Posts

Showing posts with the label Sojojin Nijar

Sojojin Nijar Za Su Gurfanar Da Bazoum Kan Zargin Cin Amanar Ƙasa

Image
Gwamnatin sojin Nijar ta sha alwashin gurfanar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan zargin babban cin amana da kuma zagon ƙasa ga sha’anin tsaron ƙasar. Masu juyin mulkin sun ce sun tattara hujjojin da za su yi amfani da su wajen gurfanar da Bazoum da kuma waɗanda suka kira muƙarrabansa na cikin gida da na ƙasashen waje. Ministan Matasa da Wasanni, Kanar-Manjo Amadou Abdraman ya sanar a talabijin a ranar Lahadi cewa za su gurfanar da Bazoum da muƙarraban nasa ne a cikin ƙasar Nijar da kuma gaban hukumomin da suka dace na duniya, kan babban cin amanar ƙasa da yin zagon ƙasa ga tsaron Jamhuriyar Nijar. Tun ranar 26 ga watan Yuli da sojojin suka yi wa Bazoum juyin mulki suke tsare da shi da matarsa da ɗansa a cikin gidansa. Shugabannin sojojin na iƙirarin cewa ba mamaye gidan nasa suka yi ba, domin kuwa yana ci gaba da mu’amala da sauran duniya, kuma likitansa na zuwa ya duba shi a kai a kai, yadda ya saba yi. Wani mashawarcin Bazoum ya tabbatar cewa a ranar Asabar