Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Umarci Dukkanin Kwamishinonin Da Zai Nada, Su Bayyana Kadarorinsu
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya umurci dukkan wadanda aka nada na kwamishinoni 19 su bi ka’idojin da’ar ma'aikata A sanarwar da babban sakataren Yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, tace, da wannan sanarwar, ana sa ran wadanda aka zaba za su bayyana kadarorinsu a cikin mafi kyawun lokaci kafin a fara tantance su a majalisar dokokin jihar a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni, 2023 da karfe 10 na safe a harabar majalisar dokokin jihar. Gwamnan ya sha alwashin cewa babu wani kwamishina da za a rantsar da shi a matsayin memba na majalisar zartaswa ta jihar ba tare da cike fom din bayyana kadarorinsa daga Ofishin hukumar kula da da'ar ma'aikata ba. "Duk sauran masu rike da mukaman siyasa a karkashin wannan gwamnati su ma za su bi umarnin da aka ba su." Gwamna Abba Kabir Yusuf na fatan jaddada aniyarsa ga mutanen jihar Kano nagari cewa gaskiya da rikon amana ya kasance tushen tsarin gwamnatinsa wanda za a yi amfani da shi wa...