Posts

Showing posts with the label Ukraine

Jirage Sun Kai Hari Kan Fadar Shugaban Kasar Rasha

Image
  Rasha ta zargi kasar Ukarine da kai harin bom da jirage marasa matuka a kan Fadar Kremlin a cikin dare. Fadar Kremlin ta yi zargin harin wani yunkuri ne a kan rayuwar Shugaba Vladimir Putin, duk da cewa Mista Putin bai samu ko rauni ba, haka ma ginin da bom sin ya samu, a harin. Fadar Kremlin ta ce Rasha na da hakkin daukar fansa a kan harin da ta kira ta’ddanci, inda ta bayyana cewa ta harbo jirage biyun da suka kai harin. Amma kakakin shugaban kasar Ukraine, Mikhaylo Podolyak, ya ce, “Ukraine ba ta da alaka da harin da aka kai wa Kremlin domin babu wata manufar sojin da haka zai cimma.” Ya yi zargin Rasha ce ta “kitsa harin domin ta samu dalilin da za ta fake da shi wajen kai harin ta’ddanci a kan Ukraine.” Kafar yada labarai ta Rasha, RIA ta bayyana cewa Mista Putin ba ya Fadar Kremilin a lokacin da aka kai harin, yana gidansa da ke Novo Ogaryovo, kuma ya ci gaba da harkokinsa yadda aka saba. Ta kuma bayyana harin a matsahin, “Yunkurin barazana ga rayuwar shugaban kasar a ranar 9

Wayar salula ce ta haddasa mutuwar sojojin Rasha 89

Image
Rundunar sojin Rasha ta ce, akwai yiwuwar sojojinta sun yi amfani ne da wayoyin salula wadanda suka bai wa takwarorinsu na Ukraine damar gano matsuguninsu har suka kai musu farmakin da ya kashe 89 daga cikinsu. Sai dai tuni Rashawa suka fara mayar wa da rundunar sojin martani da suka ce, ta fadi haka ne domin wanke kanta daga zargin sakaci. Hatta masharhanta da ke goyon bayan shugaba Vladimir Putin sun ce, watakila ma adadin sojojin da suka mutun ya zarta 89. Asarar sojoji 89, ita ce mafi girma da Rasha ta ce ta yi tun bayan barkewar yaki tsakaninta da Ukraine a cikin watan Fabairun bara. Sojojin na Rasha sun mutu ne sakamakon wani harin makami mai linzami da Ukraine ta kaddamar musu a Makiivka da ke yankin gabashin Ukraine, inda Rasha ta mamaye. (RFI)

Rasha ta ce, an kashe mata sojoji 63

Image
Rasha ta ce, an kashe mata sojoji 63 a wani kazamin hari da Ukraine ta kaddamar kan dakarunta a karshen makon da aka gudanar da bukukuwan shiga sabuwar shekara. A cikin wata sanarwa da ba a saba ganin irinta, Ma’aikatar Tsaron Rasha ta ce, an kashe sojojin kasar 63 sakamakon wani harin makami mai linzami da Ukraine ta kaddamar kan birnin Makiivka da ke gabashin Ukraine wanda Moscow ta mamaye. Wannan ne asarar sojoji mafi girma da Rasha ta yi tun bayan barkewar yaki tsakaninta da Uktraine a ranar 24 ga watan Fabairun da ya gabata. Rasha ta ce, an yi amfani da shu’umin na’urar cilla makaman roka da aka kera a Amurka wajen kaddamar mata da wannan farmakin, yayin da a Babban Hafsan sojin Ukraine ke cewa, dakarunsu ne suka kai harin a Makiivka. Ya kara daa cewa, sun lalata wuraren ajiyar makaman Rasha har guda 10 a yayin harin. Tun da fari, Sashen Yada Labarai na Rundunar Sojin Ukraine ya yi ikirarin cewa, kimanin sojojin Rasha 400 ne suka mutu a Makiivka sabanin 63 da aka ba d