Gwamnatin Kano Za Ta Tallafawa Kamfanin TC Don Bunkasa Samar Da Wutar Lantarki A Kano-Dantiye
Gwamnatin jihar Kano ta himmatu wajen yin amfani da dukkan hanyoyin da za su bunkasa samar da wutar lantarki don ci gaban masana'antu. A sanarwar da daraktan harkokin cikin gida na Ma'aikatar, Usman Bello ya sanyawa hannu, Ta tace Kwamishinan yada labarai Baba Halilu Dantiye ne ya bayyana hakan, a yayin da yake gabatar da jawabi a lokacin da ya karbi bakunci tawagar mataimakin Janaral Manaja na ofishin Kamfanin Dakon wutar lantarki dake Jahar Kano Kwamishinan ya ce Gwamna Abba Kabir a shirye yake ya ba hukumar TCN dauki domin kammala ayyukanta daban-daban a jihar. Ya kuma yi nuni da cewa, babu wata gwamnati da za ta yi watsi da damar da za ta samar da wutar lantarki ga al’ummarta, duba da irin dabarun da take da shi wajen bunkasa harkokin tattalin arziki a jihar. Daga nan sai Dantiye ya bada tabbacin GGM na goyon bayan ma’aikatar wajen fadakar da al’umma kan ayyukanta. Tun da farko a nasa jawabin, Mataimakin Janaral Manaja na shiyyar Kano Muhammad Kamal Bello ya ce...