Posts

Showing posts with the label guzuri

Karin Kudin Tikiti: Za A Dauki Dala 100 Daga Guzurin Alhazai

Image
  Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ce za ta dauki Dala 100 daga cikin kudin guzurin maniyyata aikin Hajjin bana, domin biyan karin kudin kujera da kamfanonin jiragen da za su yi jigilar su suka yi.  Yakin da ake yi a Sudan ya sa kasar rufe sararin samaniyarta, don haka dole sai jiragen da za su dauki maniyyatan su bi sabuwar hanya da ta bi ta kasar Chadi da Habasha da Eretiyiya da Kamaru kafin isa kasar Saudiyya. ِKafin barkewar yakin da ya sa aka rufe sararin samaniyyan Sudan, jiragen maniyyatan Najeriya kan tsallaka ne ta Chadi su shiga Sudan ne kadai kafin su isa Saudiyya. Wani manaja a wani kamfanin da zai yi jigilar alhazan ya bayyana wa Aminiya cewa, “A duk lokacin da aka tsayin tafiya ya karu to dole kudi su karu saboda man da za a zuba a jirgi ya karu, haka kuma kudin da za a biya ma’aikatan jirgi shi ma ya karu; Hakan ya janyo dole a yi kari a kudin tikitin alhazan.” Bayan yamutsa gashin baki da kai-kawo a tsakanin Hukumar NAHCON da kamfanonin jiragen a kan karin kudin,