Shugaba Bola Tinubu ya nada mace Shugabar Hukumar NEMA
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Zubaida Umar a matsayin Shugabar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Tarayya (NEMA). Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa Mista Ajuri Ngelale ya fitar a Yammacin wannan Juma’ar. Zubaida ita ce mace ta farko a tarihi da za ta jagoranci Hukumar ta NEMA, lamarin da ya ƙara jaddada ƙudirin Shugaban Kasar na bai wa mata dama ta damawa da su a cikin al’amuran gwamnati. Sabuwar Darakta-Janar ɗin ta NEMA tana da ƙwarewar aiki na fiye da shekaru 20 a fannoni daban-daban, ciki har da kula da gudanar da harkokin kuɗi da ma’aikata. Kazalika, mamba ce ta Cibiyar Ma’aikatan Banki ta Chartered da Cibiyar Kula da Ba da Lamuni. Misis Zubaida ta riƙe muƙamin Babbar Darektar Kula da Harkokin Kuɗi a Bankin Bayar da Lamunin Gina Gidaje na Kasa. Sanarwar ta ce an buƙaci sabuwar shugabar ta NEMA za ta kawo tsarin da ake buƙata kan harkokin kuɗi da kuma gyara hukumar a cikin ayyukan da za ta aiwatar na harkokin bayar da