Posts

Showing posts with the label Majalisar Dinkin Duniya

Adadin Mutanen Da Suka Rasa Muhalli A Sassan Duniya Ya Zarta Miliyan 114 — MDD

Image
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, adadin mutanen da suka rasa muhallansu a sassan duniya ya zarta miliyan 114, adadi mafi girma da majalisar ta tattara a tarihi. Babbar matsalar da ta raba mutanen da gidajensu a watanni shida na farkon wannan shekara ta 2023, ita ce tashe-tashen hankulan da ake fama da su a Ukraine da Sudan da Somalia da Myanmar da Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo har ma da rikici a Afghanistan. Majalisar Amurka ta yi fatali da ƙudirin janye dakarun ƙasar daga Nijar Yawan Falasdinawan da Isra’ila ta kashe a Zirin Gaza sun haura 7,000 Kazalika ibtila’o’in da aka samu na fari da ambaliyar ruwa da rashin tsaro sun taimaka wajen raba mutanen da gidajensu kamar yadda Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijra ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta bayyana. Sanarwar UNHCR ta ce, yanzu haka hankalin duniya ya karkakata ne kan yakin da ake fama da shi a Zirin Gaza wanda ya cika da dimbin fararen hula, amma fa akwai rikice-rikice da dama da ke ci gaba da ta’azzara tare da

Ta’addanci: Ba Don Taimakon Majalisar Dinkin Duniya Ba Da Mun Banu — Tinubu

Image
Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙara ɓullo da ƙwararan matakan tallafa wa Najeriya a yaƙin da take yi da ta’addanci. Tinubu ya mika wannan kokon bara ne kan abin da ya kira mummunar illar ta’addanci ga zaman lafiyar duniya da yadda yake tarwatsa mutane da ƙara haifar da fatara. ECOWAS ta musanta neman sojojin Nijar su mika wa farar-hula mulki nan da wata tara Yadda UEFA ta fitar da jadawalin Gasar Zakarun Turai ta bana Ya yi wannan kira ne lokacin da yake jawabi yayin ganawa da ƙaramin sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya kan yaƙi da ta’addanci, Mista Vladimir Voronkov, a fadar gwamnati. Shugaba Tinubu ya nunar da cewa ta’addanci ya yi ta mayar da hannun agogo baya ga harkokin ci gaban ƙasa da janyo ƙarin rashin kwanciyar hankali a tsakanin iyalai da al’ummomi Ya bayyana ce ayyukan haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya wajen tunkarar matsalar, sun kasance a tsittsinke kuma ana samun katsewar irin wannan tallafi ga ƙasashe masu tasowa. “Ya zama tilas daf
Image
Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya nemi jin matsayin shari'a daga babbar kotun duniya kan mamayen da Isra'ila ta yi wa yankunan Falasɗinawa. Ƙudurin wanda ya samu goyon bayan ƙasa 87, sai 26 suka nuna adawa da shi ciki har da Amurka da Burtaniya. Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya tana da ƙarfin yanke hukunce-hukuncen da wajibi ne a yi musu biyayya, amma ba ta iya tilasta aiki da su. Ƙuri'ar ta ranar Juma'a, ta zo ne kwana ɗaya bayan rantsar da Benjamin Netanyahu a matsayin firaminista na gwamnatin Isra'ila mafi tsaurin ra'ayi a tarihi. Isra'ila ta mamaye Gaɓar Yamma da Kogin Jordan kuma ko da yake ta janye daga Gaza amma har yanzu Majalisar Ɗinkin Duniya tana kallon yankin a matsayin wanda ke ƙarƙashin mamaye. Isra'ila na iƙirarin cewa gaba ɗayan Ƙudus ne babban birninta, yayin da Falasɗinawa ke cewa Gabashin Ƙudus ne babban birnin wata ƙasarsu da za a kafa nan gaba. Amurka na cikin tsirarun ƙasashen da suka amince da Ƙudus a matsayin babban b