Kotu Ta Tsare Dokta Idris Dutsen Tanshi A Gidan Gyaran Hali
Wata Kotun Majistare da ke Bauchi ta ba da umurnin a tisa keyar malamin addinin musuluncin nan, Dokta Idris Abdulaziz, wanda aka fi sani da Dutsen Tanshi zuwa gidan gyaran hali bisa zargin kawo hargitsi da tayar da hankalin jama’a. Majiyoyi da ga rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi da Hukumar Shari’ar Musulunci a Bauchi da kuma Almajiran malamin, sun tabbatar da tsare shi a gidan gyaran hali. A kwanakin baya ne wadansu kungiyoyin addini guda 17 karkashin kungiyar Fityanul Islam ta Najeriya, ta rubuta takardar koke ga kwamishinan ’yan sandan jihar, bisa zargin cewa Malamin ya yi batanci ga Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammadu (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi). Lamarin da ya sanya ke nan ’yan sanda suka gayyaci dukkan bangarorin da abin ya shafa kuma tun a makon jiya aka nemi malamin ya amsa goron gayyatar. Wasu daga cikin almajiransa sun bayyana cewa, Dokta Abdulaziz wanda shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi, ya amsa gayyatar ’yan sandan a ranar Litini...