Posts

Showing posts with the label Kudi

Sai Buhari Ya Yi Magana Za Mu Karbi Tsohon Kudi —’Yan Kasuwa

Image
  ’Yan kasuwa a wasu yankunan Najeriya sun bayyana cewa ba za su fara karbar tsoffin takardun N5oo da N1,000 har sai sun ji Shugaban Kasa Muhamamdu da bakinsa ya ce su fara karba. ’Yan kasuwa da kwastomominsu jihohin Kaduna da Legas da kananan hukumomin Abaji da Kwali a Yakin Babban Birnin Tarayya na kin karbar tsoffin kudin ne, a washgarin da bankunan kasuwanci suka fara bayar da su, bisa umarnin Babban Bankin Najeriya (CBN). Sai dai a Jihar Kano, harkokin kasuwanci sun fara komawa yadda aka saba, tun bayan da bankuna suka fara bayar da tsoffin kudi, kuma mutane suka ci gaba da amfani da su a harkokin kasuwanci. Harkoki sun fara kankama a Kano Wani tan kasuwa a Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, Adamu Hamza, ya ce sun fara samun karuwar ciniki,  “tsakanin jiya (Talata) da yau (Laraba), kudi ya fara yawo a hannun jama’a, suna kawowa kuma muna karba.” Aminiya ta ruwaito cewa tun ranar Talata injinan ATM a birnin Kano suka fara bayar da tsoffin kudin, sai dai yawanci N500 ne. Haka kuma an

Kotu Ta Hana Buhari Da CBN Kara Wa’adin Karbar Tsoffin Takardun Kudi

Image
  Babbar Kotun Birnin Tarayya ta hana Shugaba Buhari da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, kara wa’adin amfani da tsoffin takardun Naira da aka sauya fasalinsu. Alkalin kotun, Mai Shari’a Eleoje Enenche ya kuma hana daukacin bankuna da ke Najeriya yin duk wata hulda da ta danganci tsoffin takardun kudin ko neman kara wa’adin amfani da su daga ranar 10 ga watan 10 ga watan Fabrairu da muke ciki. Da yake sauraron ƙarar da wasu biyar daga cikin jam’iyyun siyasa 18 da ke Najeriya suka shigar, alkalin ya bukaci shugabannin bankuna da jami’ansu su kawo dalilan da za su hana a kama su da kuma gurfanar da su a gaban kotu kan zargin su da yin zagon kasa ga tattalin arziki, bisa yadda suke boye sabbin takardun Naira 1,000 da N500 da kuma N200 da CBN ya sauya wa fasali ya kuma ba su, amma suke kin ba wa mutane. (AMINIYA)