Auren Zawarawa : Gwamnatin Kano ta fara tantance ma'aurata 1800 kafin aure
Gwamnatin jihar Kano ta fara aikin tantance ma'aurata 1800 kafin a yi aure domin tantance lafiyarsu a wani bangare na sharuddan da ake bukata kafin auren. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Aminu Bello Sani ya sanyawa hannu, yace Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a lokacin da yake duba aikin a harabar hedikwatar hukumar ta Hisbah, ya ce aikin tantancewar na da nufin kaucewa kamuwa da cututtuka ga juna da kuma al’umma. Dakta Abubakar Labaran ya ce suna gudanar da gwaje-gwaje daban-daban guda 8 da suka hada da Genotype, HIV/AIDS, Hepatitis A, B da C, da syphilis da dai sauransu. Lokacin da suke cikin aikin, sun sami duk wata cuta, waÉ—anda za a iya magance su, za a iya magance su nan da nan kuma waÉ—anda ke buÆ™atar turawa za a iya tura su zuwa wani wuri don Æ™arin kulawa ko aiki. Kwamishinan ya kara da cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar za ta fitar da wata doka da za ta aiwatar da tantancewar kafin aure