Posts

Showing posts with the label Yamai

Gwamnatin Sojin Nijar Ta Tsige Shugaban ’Yan Sandan Yamai

Image
Gwamnatin rikon kwaryar Jamhuriyar Nijar ta tsige Shugaban hukumar ‘yan sandan birnin Yamai, Kwanturola-Janar Abdoulsalam Mahaman. Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda wasu daga cikin masu zanga-zangar nuna bukatar ficewar sojan Faransa ke wuce gona da iri har ma da yin fatali da doka. A jiya Litinin ne takardar tsige Kwanturola-Janar Abdoulsalam Mahaman dauke da sa hannun Ministan Cikin Gida, Janar Mohamed Toumba ta fara karade kafafen sada zumunta, wacce wata majiyar sabbin hukumomin na Nijar ta tabbatar wa Muryar Amurka da sahihancinta. A ranar Larabar da ta gabata ne Mahaman ya gargadi masu zaman dirshan a harabar sansanin sojan Faransa da ke dab da filin jirgin saman Yamai da su koma gefen titi domin bai wa masu ababen hawa damar kai da kawo ba tare da wata tsangwama ba. Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda wasu daga cikin wadanan mutane ke uzzurawa masu ababen hawa da suke tilasta cire belt ga masu motoci ko hular kwan...