Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano Ta Kammala Shirye-Shiryen Aikin Hajjin 2024 - Laminu Rabi'u Danbappa
Shugaban Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Yusif Lawan, ya bayyana a yau Laraba cewa sun samu nasarar kammala dukkan shirye-shiryen aikin hajjin 2024 a kasar Saudiyya. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Wannan sanarwar ta zo ne a yayin gabatar da kayayyakin bulaguro bayan taron hukumar da aka gudanar a dakin taro. Alhaji Yusif Lawan ya jaddada kudirin hukumar na ganin an shirya tsaf da kuma tashi zuwa aikin hajjin a kan kari, sakamakon tsare-tsaren masu inganci da suka yi. An kula da kowane fanni na aikin hajji, tun daga kaya na hannu zuwa inufom din maza da mata, da hijabi na alhazai mata, da littafan jagororin aikin Hajji, wanda hakan ya baiwa alhazan Kano damar gudanar da tafiyarsu ta alfarma da kwarin gwiwa da kwanciyar hankali. A nasa jawabin Darakta Janar na hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya yabawa shuwagabannin da suka sa i...