Posts

Showing posts with the label Muhalli

Adadin Mutanen Da Suka Rasa Muhalli A Sassan Duniya Ya Zarta Miliyan 114 — MDD

Image
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, adadin mutanen da suka rasa muhallansu a sassan duniya ya zarta miliyan 114, adadi mafi girma da majalisar ta tattara a tarihi. Babbar matsalar da ta raba mutanen da gidajensu a watanni shida na farkon wannan shekara ta 2023, ita ce tashe-tashen hankulan da ake fama da su a Ukraine da Sudan da Somalia da Myanmar da Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo har ma da rikici a Afghanistan. Majalisar Amurka ta yi fatali da ƙudirin janye dakarun ƙasar daga Nijar Yawan Falasdinawan da Isra’ila ta kashe a Zirin Gaza sun haura 7,000 Kazalika ibtila’o’in da aka samu na fari da ambaliyar ruwa da rashin tsaro sun taimaka wajen raba mutanen da gidajensu kamar yadda Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijra ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta bayyana. Sanarwar UNHCR ta ce, yanzu haka hankalin duniya ya karkakata ne kan yakin da ake fama da shi a Zirin Gaza wanda ya cika da dimbin fararen hula, amma fa akwai rikice-rikice da dama da ke ci gaba da ta’azzara tare da