Jami’ar Maiduguri Za Ta Kafa Gidan Tarihin Tunawa Da Rikicin Boko Haram
Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas ta ce tana aiki da Jami’ar Maiduguri domin kafa gidan tarihin tunawa da rikicin Boko Haram a yankin. Shugaban hukumar, Mohammed Alkali ne ya bayyana hakan ranar Alhamis, inda ya ce kafa gidan zai taimaka wajen bayar da tarihin rikicin ta yadda zai canza tunanin mutane kuma ya amfane su. Ya bayyana hakan ne yayin bikin Ranar Zaman Lafiya ta Duniya ta 2023 a Maiduguri. Alkali ya kuma ce gidan zai ba masu ruwa da tsaki damar su samar da bayanai masu kyau da za su sa mutane su fahimci illar yaĘi a kan yankin da ma kasa baki Éaya. Ya ce kofar hukumar a bude take domin kowanne irin kokarin da zai taimaka wajen daĘile ayyukan ta’addanci da tayar da Ęayar baya a yankin. Tun da farko sai da shugaban kungiyar Jakadun Kungiyar Bunkasa Zaman Lafiya da Dogaro da Kai, Ahmed Shehu, ya nuna wa Alkali wasu ayyukan kirkira da wasu matasa da ba sa zuwa makaranta suka yi. A nan ne shugaban ya nuna gamsuwarsa da kirkire-kirkiren, inda ya ce za su yi nazari a...