Posts

Showing posts with the label Rance

Shafin Karbar Rancen Karatu Zai Fara Aiki Ranar Juma’a —Gwamnati

Image
A ranar Juma’a mai zuwa za a bude shafin neman rancen kudin karatu da Gwamnatin Tarayya ta bude domin dalibai zai fara aiki. Manajan Daraktan Asusun Lamunin Karatu na Najeriya (NELFUND) Mista Akintunde Sawyerr ne ya bayyana 24 ga Mayu, 2024 a matsayin ranar bude shafin neman rancen kudin karatun ga dalibai. Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Alhamis. Ya ce masu buƙatar rancen za su iya shiga shafin ta www.nelf.gov.ng domin neman wani agaji kuma sai su tuntubi hukumar asusun ta info@nelf.gov.ng. Ya ce: “Ta shafin, dalibai za su iya samun rance kudin makaranta ba tare da damuwa ba.” Sanarwar da ke dauke da sa hannun mai kula da harkokin yada labarai da hulda da jama’a na asusun, Nasir Ayitogo, ta ce shafin samar da rancen na da saukin sarrafawa kwarai da gaske. Manajan Daraktan Asusun Lamunin karatun Najeriya ya shawarci wadanda suka cancanci wannan tallafi su gaggauta cikewa domin su mori tsarin da zai taimaka wa gobensu. (AMINIYA)

Gwamnatin Tarayya ta ce daga watan Satumbar wannan shekara za ta fara ba wa dalibai rance-Mashawarcin Shugaban

Image
Mashawarcin Shugaban Kasa kan Ayyuka na Musamman, Dele Alake, ya kara da cewa gwamnati za ta bullo da sabbin hanyoyin tallafa wa dalibai masu karamin karfi. “Daga cikin abubuwan da gwamnatin ta tsara na tabbatar da ganin kowane dalibi ya kammala karatunsa a kan lokaci, komai karamin karfin iyayensa, akwai daukar su aikin wucin gadi a makarantunsu, bayar da rance da kuma daukar nauyin wadanda suka cancanta a cikinsu,” a cewarsa. Alaka ya ce dokar bai wa dalibai rance da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu za ta fara aiki gabanin shiga sabuwar shekarar karatu mai kamawa a watan Satumba . Sai dai kuma bai ce uffan ba game da matakai ko shirye-shiryen da gwamnatin ta yi domin tabbatar da hakan. Ya kuma  nesanta Gwamnatin Tarayya da karin kudin rajista da sauransu da jami’o’inta suka yi, inda ya ce, har kwanan gobe ba a biyan kudin makaran a jami’o’in, don haka babu gaskiya a rahoton da wasu kafofin yada labarai suka wallafa cewa gwamnatin ta kara kudin makaranta a jami’o’inta....

Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Dokar Baiwa Dalibai Rance

Image
Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya rattaba hannu a kan dokar da za ta bai wa daliban manyan makarantu bashi su yi karatu, su biya daga baya. Mamba a rusasshen Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Dele Alake ne ya sanar da hakan ranar Litinin. Ya ce za a rika adana kudaden da za a yi amfani da su wajen aiwatar da shirin ne a lalitar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, kuma za a rika bayar da su ne kawai ga daliban manyan makarantu masu karamin karfi. Kudurin dokar dai, ainihi Kakakin Majalisar Wakilai ta tara, Femi Gbajabiamila ne ya gabatar da shi, kuma ya tsallake karatu na uku ne makonni biyu da suka gabata. Dokar dai ta tanadi bayar da bashi mara ruwa ga daliban manyan makarantu marasa karfi ta hanyar Asusun Tallafa wa Ilimi na Najeriya. (AMINIYA)