Posts

Showing posts with the label Hukumar zabe

Hukumar Zabe Ta Sanar Da Abba K Yusuf A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kano

Image
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam'iyar NNPP  a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano da aka kammala kwanan nan da kuri'u 1,019,602.

Kofa Ya Gudanar Da Taron Addu'a, Godiya Da Kuma Sako Ga Jami'an Tsaro Da Hukumar Zabe

Image
A ranar Asabar ce sabon zababben dan majalissar tarayya mai wakiltar Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa PhD, ya jagoranci Sallar Nafila tare da addu'oi da godiya ga Allah da al'umma bisa nasara da Allah ya bashi a zaben da ya gabata  Haka kuma an gudanar da addu'oi na musamman wa mai girma Madugu Sen Rabiu Musa Kwankwaso da addu'oin samun nasarar Engr Abba Kabir Yusif da yan takararsu na majalisar jiha a Bebeji da Kiru da kano a zabe mai zuwa. A hanu guda kuma Kofa ya kaddamar da tsare tsare na musamman akan zabe mai zuwa kuma yayi kira da babbar murya ga jami'an tsaro da ma'aikatan zabe wanda aka turo su Kano, akan su tabbatar sun tsaya akan gaskiya don samun zaman lafiya a kano

Bamu kai Karar Shugaban INEC Kotu ba - DSS

Image
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta musanta labarin da ke yawo cewa tana cikin hukumomin tsaron da suka maka Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu a kotu. Kakakin rundunar, Peter Afunanya ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai, inda ya yi karin haske kan umarnin wata Babbar Kotun Abuja na hana hukumomin tsaro ciki har da DSS din kama Yakubu. Boka ya mutu yana lalata da matar fasto Mun gano wadannin macizai a dajin Ecuador —Masana A ranar Laraba ce dai Alkalin Kotun, M. A. Hassan ya ki amincewa da bukatar tsige shugaban INEC din daga mukaminsa, saboda zargin kin bayyana ainihin kadarorin da ya mallaka. Alkalin ya ce kadarorin da Yakubun ya bayyana haka suke, kuma sun yi daidai da tanadin dokokin Najeriya. Hukuncin dai ya biyo bayan karar da Somadina Uzoabaka ta shigar da Babban Lauyan Gwamnatin da Farfesa Yakubu mai lamba FCT/HC/GAR/CV/47/2022 don tilasta wa shugaban hukumar ta INEC sauka daga matsayinsa, har sai an gudanar da binciken wasu

Duk wanda ba shi da kuri'a ba zai yi zabe ba - INEC

Image
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta jaddada cewa babu wanda zai kada kuri'a a zaben 2023 mai zuwa sai mai katin zabe  Jami'in zabe na karamar hukumar Gwarzo Mal.Bello Ismail ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki a ofishinsa.  Bello Ismail ya kara da cewa an samar da sabbin rumfuna saba'in da uku domin rage cinkoso da masu kada kuri'a sama da dubu daya a Gwarzo,Getso,Kutama,Lakwaya,Mada da ,Unguwar tudu dake karamar hukumar Gwarzo.  Jami’in zaben ya kuma kara da cewa INEC za ta kai unguwanni goma na kananan hukumomin domin rabon kaya daga ranar 6 ga watan Janairu zuwa 15 ga watan Janairu. Da yake jawabi a wajen taron sakataren jam’iyyar A.P.C. Samaila Abdullahi ya shawarci hukumar zabe da ta kaucewa tarin pVC na uku. A nasu jawabin jami'in 'yan sanda DSS, da Civil Defence kira suka yi INEC da su bayar da motocin daukar kayan zabe da jami’ai domin kaisu wuraren da ya dace.  Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da wakilan babban l