Posts

Showing posts with the label Hukumomin Alhazai

Hajj 2024: NAHCON Ta Baiwa Hukumomin Alhazai Na Jihohi Wa'adin Sanya Kudaden Maniyyatansu

Image
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta yi kira ga Jihohin kasar da su gaggauta fitar da kaso mai tsoka na kudaden da suka dace domin samun gurbin da aka ware wa Jihohinsu.   A wata wasika da daraktan kudi da asusu Dr. Salihu ya aikewa shugabannin hukumomin jin dadin alhazai da hukumomi da kwamitocin jiha. A. Usman ya bayyana cewa kiran ya zama wajibi bisa la'akari da wa'adin da Ma'aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fitar wanda ya wajabta wa duk wani mai niyyar zuwa aikin Hajji na 2024 ya fitar da kudadensa kafin wani lokaci.   A cewarsa, rashin bin umarnin za a fassara shi da cewa ba shi da shiri ko kuma ba shi da sha’awar shiga aikin Hajji na 2024.   Ya kuma bayyana cewa rashin bin wannan umarni zai bar Hukumar ba ta da wata hanya ko zabi illa rage rabon irin wadannan Jihohin da kuma raba wa Jihohin da suka kammala turawa da kuma bukatar karin gurbi.   Ya yi nuni da cewa yana da matukar muhimmanci a samar da isassun kudade na asusun IBAN na Hukumar na...