Search This Blog

Showing posts with label Kungiyar Kwadago. Show all posts
Showing posts with label Kungiyar Kwadago. Show all posts

Wednesday, 15 May 2024

Kungiyar Kwadayo Ta Yi Watsi Da Naira 48, 000 A Matsayin Mafi Karancin Albashi

Ƙungiyar Ƙwadago NLC ta yi fatali da tayin naira 48,000 da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata a ƙasar.


Mambobin ƙungiyar ta NLC a wannan Larabar su bayyana mamakin dalilin da gwamnati da mambobin kamfanoni masu zaman kansu ke tozarta su da abin da ta bayyana a matsayin tayi mai ban dariya.


Aminiya ta ruwaito cewa a yayin da Gwamnatin Tarayya ta miƙa tayin Naira 48,000, ‘yan ƙungiyoyi masu zaman kansu sun miƙa tayin N54,000.


Sai dai ƙungiyar NLCn ta bayyana adawartwa kan duk tayin da ɓangarorin biyu suka gabatar a wani taron tattaunawa da aka gudanar a babban Ofishin NLC na Labour House da ke Abuja.


Shugabannin ƙwadagon sun ce gwamnati ba ta gabatar da wasu bayanai da za su goyi bayan tayin da ta gabatar ba.


Wednesday, 15 November 2023

Labari da dumiduminsa: Kungiyar Kwadago ta janye yajin aikin da ta fara gudanarwa

Kungiyar Kwadagon ta kasa ta Janye yajin aikin ne bayan zaman tattaunawar da mai bawa Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu

Cikakken labarin zai zo muku nan gaba 

Wednesday, 26 July 2023

Kungiyar Kwadago Ta Kasa Za Ta Fara Gudanar Da Yajin Aiki

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki bakwai da ta sauya duk wasu manufofin da ake ganin na yaki da talakawa, ciki har da karin farashin man fetur da aka yi a baya-bayan nan, ko kuma ta fuskanci yajin aikin gama gari daga ranar 2 ga watan Agusta.

Kungiyar kwadago ta NLC ta umurci dukkanin kungiyoyin ta da kuma majalisun jihohi da su gaggauta fara shirin daukar ma’aikata da sauran ‘yan Najeriya da suka hada da kungiyoyin farar hula don gudanar da yajin aikin da za a dade da gudanar da zanga-zanga idan har gwamnati ta gaza biyan bukatunta.

Jaridar Nigerian Tracker ta rawaito cewa wannan na daya daga cikin shawarar da aka cimma a taron kwamitin tsakiya na NLC, CWC, wanda aka gudanar a ranar Talata, 25 ga watan Yuli, a gidan ma’aikata na Abuja.

Cikakken labarin zai zo muku nan gaba 

Wednesday, 31 May 2023

Za Mu Yi Fito-Na-Fito Da Gwamnati Kan Cire Tallafin Man Fetur - Kungiyar Kwadago

Kungiyar kwadagon Najeriya ta sha alwashin yin fito na fito da gwamnatin kasar a kan yunkurin da sabon shugaban Najeriyar ke yi na janye tallafin mai.

Kungiyar ta ce ba za ta amince ba, saboda janye tallafin zai jefa al'umma a cikin wahala.

Tun bayan sanarwar da shugaba Tinubu ya yi a ranar da aka rantsar da shi aka fara dogayen layukan mai a sassan kasar.

Kwamarade Nasir Kabir shi ne sakataren tsare-tsare na Kungiyar NLC ya shaida wa BBC cewa shugaban Najeriyar ya yi hanzarin sanar shirin cire tallafin man fetur ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba.

"Kafin ka janye tallafi sai ka kawo wutar lantarki, tituna duk sun wadata talakawa sun rabu da talauci a kasa, ake maganar gwamnati ba ta hannu a cikin wannan abu", in ji shi.


Kungiyar ta yi ikirarin a cikin sa'o'i bayan sanarwar shugaban kasa alummar kasar sun tsinci kansu cikin wani hali na tsaka mai wuya saboda an fuskanci karancin man fetur a wasu sassan kasar da karin farashin mai inda a wasu wurare gidajen mai farashin man fetur din ya karu da kashi 300 cikin 100.

Mahukuntan kasar sun sha ikirarin cewa wasu tsiraru ne ke amfana da tallafin man, don haka yakamata a cire shi .

To sai dai NLC ta yi watsi da haka kamar yada Kwamarade Nasir Kabir ya bayyana:

"Duk wannan magana ne ina tabbatar maka tatsuniya ce, ba mu gamsu da shi ba, ai maganar gaskiya shi ne me ya sa su gwamnatin da ta shigo da ke son ta janye wannan tallafi, da mun zauna mun nuna mu su aubuwan da ke kasa, sai su gane cewa mun fi su gaskiya sai su fasa", in ji shi.

Kungiyar kwadagon ta ce tana adawa da wannan mataki na shugaba Tinubu kuma ta nemi gwamnati da ta janye shirin cikin gaggawa.

NLC ta kuma yi ikirarin cewa abubuwan da wannan mataki zasu haifar za su yi illa ga fanin tsaro da walwalar jama’a.

Hon Abubakar Yunus ɗan majalisar wakilai daga Gombe ya shaidawa BBC cewa dawainiyar ta fi karfin gwamnati, kuma talakawa ba sa amfana da tallafin man.

"Ai mun jima muna kira ga tsohon shugaban kasa Muhamadu Buhari da lallai ya janye tallafin.

"Mun kawo korafe korafe a kan cewa tallafin nan in banda cutar da jama'ar da suke kuka a yanzu, ai gara ma a cire shi.

"Da sun san badakalar da babakere da ake yi mu su a wannan harka ta subsidy,…ko da za su yi azumin wata guda da sun amince a cire shi".

Batun janye tallafin dai a yanzu shi kowa ke tattaunawa a kai, fatan 'yan Najeriya dai shi ne samun rangwame daga hauhawa farashin da wasu ke ganin babu mamaki ya karu da wannan sabon tsari.

BBC Hausa 

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...