Shugaban NAHCON Ya Yabawa Kungiyar AHUON Tare Da Bada Shawarar Horar Da Wakilansu
Mai rikon Shugabancin Hukumar Alhazai ta Najeriya, Malam Jalal Ahmad Arabi, OON, fwc, l ya yaba da gagarumin kokarin da kungiyar masu gudanar da aikin Hajji da Umrah ta Najeriya (AHUON) ke yi na shirya aikin Hajjin bana na 2024 ba tare da matsala ba ta hanyar horar da mambobinta kan sabon tsarin shirin. Shugaban ya bayyana haka ne a taron karawa juna sani da kungiyar AHUON ta shirya a Otel din Immaculate dake Abuja. Shugaban wanda ya kasance babban bako a wajen taron, ya jaddada bukatar samar da kyakkyawar alaka tsakanin NAHCON da kungiyar domin ganin Alhazai sun samu sauki A sanarwar da Mataimakin daraktan yada labarai na hukumar, Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace Shugaban wanda ya samu wakilcin Daraktan sa ido da bin ka’ida, Alhaji Alidu Shittu, ya yabawa kokarin mai shirya taron na bayar da horon da nufin karawa mambobinsu ilimin sabbin ci gaba a aikin Hajji tare da yin kira gare su da su shiga cikin sabuwar Cibiyar bayar da horo kan ayyukan Hajji da Hukumar t...