Search This Blog

Showing posts with label Yashi. Show all posts
Showing posts with label Yashi. Show all posts

Monday, 20 May 2024

Gwamnatin Kano Ta Umarci Shugabannin Kananan Hukumomi Su Rinka Kai Rahoton Duk Wuri Da Ake Hakar Kasa Ko Yashi Ba Bisa Ka'ida Ba

Kwamishinan ma'aikatar kasa da tsare-tsare ta jahar Kano, Alhaji Abduljabbar Mohammed Umar ya bayyana hakan ga manema labarai bayan karbar koken al'ummomin kananan hukumomiin Gezawa da Gaya da Bebeji da Dawakin Tofa, akan yadda ake hakar kasa a yankunansu ba bisa ka'ida ba.

Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin Kano ta lura  da cewa wasu kamfanoni da suke hakar kasa a garuruwan Chediya Ingawa da Kalebawa a karamar hukumar Dawakin Tofa, wanda gwamnati ta basu umarnin dakatawa, da hakar kasar sun dawo sun ci gaba da aikin hakar kasar bisa zargin suna samun goyon baya daga sama.

Abduljabbar ya kuma kara da cewa a doka gwamnatin Tarayya ita ta ke bada izinin hakar kasa ko ma"adanai, haka kuma Dokar ta baiwa Gwamnatin Jaha ikon sahalewa tare da izinin Gwamna, da izinin shugaban karamar hukuma, da kuma al'ummomin garuruwan da abin zai shafa.
Kwamishinan ya kuma zayyano sharudan da doka ta tanadar kafin fara aikin hakar kasa ko ma'adanai. "Insert"
Abduljabbar Mohammed ya kuma tabbatarwa da al'ummar jahar Kano cewa Gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf ba za ta nade hannunta kuma ta zuba Ido ana cutar da al'ummarta ta bari ba, za ta yi duk abin da ya dace bisa doran doka don kare mutuncin Al'ummar  jahar Kano.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...