Posts

Showing posts with the label Man Fetur

Gwamnatin Kebbi Za Ta Raba Man Fetur Kyauta Ga Manoma

Image
Gwamnatin Kebbi ta bullo da shiri na musamman domin raba man fetur kyauta ga manoman rani da nufin saukaka musu yin wahalar noma a jihar. Kwamishinan Noma na jihar, Shehu Mu’azu ya ce gwamnatin ta samar da haujin noma, inda aka farrfado da aikin noma domin jihar ta cigaba da rike kambunta a bangaren noman shinkafa a Nijeriya. Saboda haka ne ta gina karamin wurin noma na zamani a kananan hukumomin Argungu da Fakai a garin Mahuta. Wannnan a cewarsa, kari ne a kan tallafin noman rani da manoman shinkafa 30,000 da masu noma masara 7,500 da kuma masu noman rogo 2,000 suka samu daga gwamnatin. (AMINIYA)

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Yi Kira Ga Masu Gidajen Man Fetur Dasu Dasu Siyar Da Mai A Tsohon Farashi

Image
Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusif ya bukaci ‘yan kasuwar man fetur da su dawo da farashin man fetur na baya domin rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta a halin yanzu. A sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, tace Gwamnan ya ce yana sane da cewa har yanzu ‘yan kasuwar na da tsohon man fetur da ya kamata a sayar da shi a tsohon farashi. Domin rage wahalhalun da ‘yan jihar ke fama da su, ya kamata ‘yan kasuwa su yi hakuri su sake bude duk gidajen mai da kayayyakin da ake da su a hannun jari don sayarwa a kan tsohon farashi. “A matsayina na Gwamna, na ji takaicin ganin yadda Al’ummarmu na Kano ke shan wahala sakamakon hawan man fetur da bai dace ba, kuma dole ne a kawo karshen lamarin nan take.” Inji Gwamnan. Kano a cewar Gwamna Abba Kabir, ita ce cibiyar kasuwanci a yankin arewacin kasar da kuma wasu kasashe a yammacin Afirka, kuma al'ummarta masu tarin yawa na ci gaba da samun kyakkyawan yanayin kasuwanci. ...

Akwai yiwuwar a soma cire tallafin fetur a watan Afrilu - Gwamnatin Najeriya

Image
  Akwai yiwuwar gwamnatin tarayyar Najeriya ta soma cire tallafin man fetur daga Afrilun 2023, wato watanni uku kafin yadda ainahin lokacin da aka yi niyyar cire tallafin a baya. Ministar kuÉ—i da kasafi Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a wata hira ta musamman da ta yi da gidan talabijin na Arise a yayin wani taro na tattalin arzikin duniya a Switzerland. "Abin da ya fi shi ne wannan gwamnatin watakila ta soma cire tallafi a farkon zango na biyu na wannan shekara saboda zai fi nagarta idan aka cire a hankali a maimakon a jira a cire shi baki É—aya," in ji ministar. Ta bayyana cewa duka Æ´an takarar shugaban Æ™asar Najeriya a lokutan yaÆ™in neman zaÉ“ensu duk suna da ra'ayin cire wannan tallafin Bayan Æ™ara wa'adin watanni 18, gwamnatin tarayya ta shirya kashe naira tiriliyan 3.35 kan tallafin mai daga Janairu zuwa Yunin 2023. Wannan Æ™arin wa'adin da aka yi ya janyo muhawara matuÆ™a kan irin kuÉ—in da za a kashe sakamakon ana ganin cewa zai Æ™ara giÉ“i a kasafin kuÉ—i wanda kum...

A Watan Maris Za A Fara Hako Man Fetur A Jihar Nasarawa – NNPC

Image
Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) ya ce a watan Maris Mai zuwa zai fara aikin hako danyen man fetur a karo na farko a Jihar Nasarawa. Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya bayyana hakan ranar Juma’a, lokacin da ya karbi Gwamnan Jihar, Injiniya Abdullahi Sule da kuma wata tawaga daga Jihar a ofishinsa. Gano man a rijiyar Keana ta Yamma da ke Jihar ta Nasarawa na zuwa ne kasa da wata biyar bayan kamfanin ya fara hakar wani a rijiyar Kolmani da ke tsakanin Jihohin Bauchi da Gombe. A cikin sabuwar sanarwar da ya fitar ranar Juma’a, NNPC ya ce, “A ci gaba da aikinsa na gano man fetur a yankunan tsandauri na Najeriya, kamfanin zai fara aikin hako mai a rijiya ta farko a Jihar Nasarawa a watan Maris na 2023.” Jaridar Aminiya ta ruwaito} Mele Kyari ya ce sakamakon binciken da suka gudanar ya tabbatar da akwai man fetur din dankare a yankin. Daga nan sai ya bukaci a gaggauta fara aikin saboda ya ce sannu a hankali duniya ta fara dawowa daga rakiyar man fetur zuwa makamashin da ba ya lal...

Za a shafe wata shida nan gaba cikin karancin Fetur a Najeriya - Inji IPMAN

Image
Kungiyar dillalan man fetur a Najeriya ta ce za a ci gaba da fuskantar karancin fetur a faɗin kasar har zuwa watan Yunin wannan shekarar. Kungiyar ta ce wahalhalun ko karancin na da alaƙa da shirin gwamnati na janye tallafin mai baki daya a cikin watan Yuni. Tun a shekarar da ta gabata al'ummar kasar ke fama da karanci mai a sassa daban-daban na Najeriya, musamman arewaci. A ranar Litinin ministan albarkatun fetur, Timipre Sylva, ya ce kamfanin mai na NNPC na tafka asara kan farashin da ake sayar da man a yanzu. A makon da ya gabata, ministan kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ya ce gwamnatin Tarayya ta ware naira tiriliyan 3.6 domin biyan tallafi zuwa Yunin 2023.

Gwamnatin tarayya za ta dena biyan tallafin man Fetur

Image
  Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce daga Æ™arshen watan Yunin wannan shekara za ta daina biyan tallafin man fetur a Æ™asar. Ministar kuÉ—i, kasafi da tsare-tsare ta Æ™asar Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a lokacin gabatar da kasasfin kuÉ—in shekarar 2023. BBC Hausa ta rawaito cewa Misis Zainab ta ce gwamnatin tarayya ta ware kimanin naira tiriliyan 3.36 domin biyan tallafin man fetur É—in a cikin wata shida na farkon shekarar 2023. Ministar ta Æ™ara da cewa hakan na daga cikin tsarin tsawaita cire tallafin zuwa wata 18 da gwamnatin ta bayyana a shekarar da ta gabata.