Posts

Showing posts with the label Sarkin Kano

Labari Da Dumiduminsa: Sarki Sanusi Ya Isa Gidan Gwamnatin Kano, Gabanin Zuwansa Fadarsa

Image
Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi, ya isa gidan gwamnatin Kano domin karbar takardar nadinsa a hukumance tare da ci gaba da aikinsa a matsayin Sarki   Aminiya ta rawaito cewa Sarkin ya isa Kano da yammacin ranar Alhamis kuma an shirya masa liyafar maraba da zuwa gida sakamakon shawarwarin tsaro. An dai shirya taron da ake sa ran zai tunkari mai martaba Sarkin wajen fitowar sa na farko a bainar jama'a tun bayan da aka dawo da shi kan karagar mulki. Ana sa ran zai kasance a dakin taro na Africa House da ke gidan gwamnatin Kano domin gudanar da bikin karamar durbar da karfe 10 na safe, inda zai wuce fadar gidan Sarki na Nassarawa. Daga nan ne Sarkin zai ci gaba da jagorantar sallar juma’a a babban masallacin Kano da ke fadar a kofar Kudu.

Sarkin Kano Ya Bukaci Gwamnati Ta Samar Da Wata Hanyar Da Al'uma Zasu Samu Saukin Rayuwa

Image
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci hakan ne lokacin da ya kai ziyarar barka da sallah gidan Gwamnatin jihar Kano a hawan Nassarawa da ya gabatar yau Lahadi a cigaba da gudanar da haye hayen sallah karama. A sanarwar da babban sakataren yada labaran Sarkin, Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya sanyawa hannu, Sarkin yace sakamako matsin rayuwa da ake fama da ita akwai bukatar Gwamnati da mawadata su tallafawa marasa shi domin samun saukin gudanar da al'amuran rayuwarsu. Ya kuma tunasar da al'uma shirin gwamnati na Kidayar al'uma da za'a gudanar a dukkanin fadin kasar nan inda ya bukaci al'uma dasu tabbatar an kidayasu a lokacin gudanar da aikin kidayar. Mai Martaba Sarkin godewa Gwamnatin jihar Kano bisa kokarinta na samar da Tsaro da Zaman lafiya inda ya godewa Malamai da limamai wajan gudanar da addu'oi domin dorewar Zaman lafiya a jihar Kano. Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga al'uma su cigaba da baiwa gwamnati goyon baya yace duk wasu aikace aikac...

Kuyi amfani da kalaman da al'uma zasu gamu dasu wajan yakin neman zabe: Mai Martaba Sarkin Kano.

Image
Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ad Bayero ya yi kira ga masu neman kujerun mulkin kasar nan da su tabbatar sunyi kalamai da al'umma za su gamsu da su wajen neman kuri'ar alumma a zaben shekarar 2023. A sanarwar da Sakataren yada labaran Masarautar Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya sanyawa hannu, ta ce Sarkin ya bayyana haka ne lokaci da dan takarar shugaban kasa na jam'iyar SDP Adewale Adebayo da dantakar kujerar gwamnan jihar Kano Dr. Muhammad Bala gwagwarwa yayin da su ka  ziyar ce shi a fadar sa. Alhaji Aminu Bayero, ya kuma nemi da duk wani dake neman kujerar da yasan cewa Allah ne ke bayar da Mulki bawai karfin ikon tada zaune tsayeba. Da yake nasa jawabin, dan takarar Gwamna na jam'iyyar ta SDP Bala Muhammad Gwagwarwa ya ce sun ziyarci fadar sarkin ne domin neman tabaraki da addu'ar. A wani cigaban kuma Martaba Sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya nada Dr. Malam Umar Ibrahim Indabawa  a matsayin sabon limamin  Masallacin Darul hadis dake Ung...

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Ya yi sabon Aure

Image
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya auri mata ta biyu Hauwa'u Adamu Abdullahi Dikko a Kano ranar Juma'a. Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa an gudanar da daurin auren  ne a gidan marigayi Jarman Kano Farfesa Isah Hashim da ke unguwar Nasarawa GRA a cikin babban birnin tarayya. Sannan kuma Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabahani Ibrahim ne ya wakilci Mai Martaba Sarkin a lokacin daurin auren, yayin da Alhaji Shehu Hashim ya kasance waliyin  amarya.

MAI MARTABA SARKIN KANO ALHAJI AMINU ADO BAYERO: Baƙon Shehu Maghili

Image
Daga: Magaji Galadima A ranar Litinin 12 ga watan Disamba 2022 gwamnatin Æ™asar Aljeriya ta aiko da wani jirgi na musamman domin ya É—auki mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zuwa Æ™asar ta Aljeriya domin halartar taron duniya na musamman don tunawa da rayuwa da kuma aiyukan shahararren malamin addinin Musulunci sharifi kuma masanin falsafa  wato Shehun malami Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a Æ™arni na goma sha biyar.  Jigin ya tashi daga Kano da karfe 9:45 na safe. A cikin waÉ—anda suka samu alfarmar raka Sarki wannan tafiya akwai Sarkin Dawakin Tsakar-gidan Kano Alhaji Ahmad Ado Bayero hakimin Kumbotso da Ambasada Ahmad Umar ÆŠanmalikin Kano da Dakta Ibrahim ÆŠahiru Bauchi wanda ya wakilci Sheikh ÆŠahiru Bauchi da Malam Isa Sanusi Bayero da Dakta Lawi Atiku Sanka da kuma ni Magaji Galadima Kachallan Kano, sannan sai wasu malamai da sharifai na Kano da kuma fadawa hadiman Sarki.  Jirgin ya É—an yada zango a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nija...