Posts

Showing posts with the label Maniyyata Hajjn 2024

Maniyyata 51,447 Suka Biya Kudin Hajin 2024 - NAHCON

Image
  Bayan rufe biyan kudin Hajji, adadin maniyyatan da suka yi rijistar zuwa aikin hajjin 2024 daga Najeriya ya kai 51,447 a karkashin kason gwamnati. A sanarwar da mataimakiyar daraktar harkokin hulda da jama'a ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace abin yabawa ne, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta taka rawar gani wajen ganin an cimma wannan kyakkyawar manufa. Hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta amince da sadaukarwa da dama da gwamnatin tarayya ta yi a kan duk wata matsala da ta taso wajen ganin an samu saukin matsalolin da ke addabar maniyyata. Hukumar ta kuma yaba da hakurin da mahajjata suka nuna a cikin rashin tabbas. Damuwar da Malamai suka nuna kan halin da Alhazai ke ciki bai wuce Hukumar ta lura da shi ba. Masu ruwa da tsaki da dama, ciki har da Gwamnonin Jihohi, sun ba da mafita daga halin da aka tsinci kai. Wasu kafafen yada labarai sun nuna matukar fahimtar matsalolin da a zahiri suka fallasa gaskiyar lamarin da Hajjin 2024 ke fuskanta. Hakika shir...