Posts

Showing posts with the label Shan giya

Hisbah Ta Rufe Wuraren Shan Giya Sama Da 100 A Zariya

Image
Wata kungiyar addinin Musulunci mai zaman kanta mai suna Hisbah, ta jagorance garkame wuraren shan giya sama da 100 a Karamar Hukumar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna. Dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Sabon Gari, Garba Datti Babawo ne ya tabbatar da hakan, yayin gabatar da hsaidar kammala karbar horo ga ’yan kungiyar su 750 da ya gudana a hedkwatar Karamar Hukumar ta Sabon Gari. Dan majalisar ya ce tun da Karamar Hukumar take ba ta taba samun sa’ida daga ayyukan badala ba sama da lokacin da aka kafa rundunar ta Hisbah. Daga nan sai Babawo ya ja kunnen dakarun da su tabbatar suna bin dokokin dokoki yayin gudanar da ayyukansu. Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar ta Sabon Gari, Injiniya Mohammed Usman, ya jaddada kudurin gwamnatinsa na kakkabe yankin daga ayyukan masha’a, ta yadda za a sami yanayin kasuwanci mai kyau tare da bunkasa zaman lafiya a tsakanin al’umma. Tun da farko sai da Kwamandan rundunar a yankin, Abubakar Auwal ya ce dakarun su 750 su...