Gwamna Abba Kabir Ya Yi Bankwana Da Tagwayen Da suka hade Da Za Ayi Tiyatar Rabasu A Saudiyya
....Ya yabawa Masarautar Saudiya bisa kara kaimin agaji ga Kano Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yabawa masarautar Saudiyya karkashin jagorancin Sarki Salman Bin Abdul'aziz kan daukar nauyin yi wa jarirai tagwaye a Kano tiyata a wani asibiti da ke kasar Saudiyya a birnin Riyadh. Da yake jawabi a lokacin da yake bankwana da iyayen tagwayen jarirai a filin jirgin sama na Aminu Kano, gwamnan ya bayyana irin alherin da Sarki Salman ya yi a matsayin wani aiki da Allah ya saka masa da ya dace a yi koyi da shi. Gwamna Yusuf wanda ya yi addu’ar Allah ya dore da dankon zumuncin da ke tsakanin Kano da Masarautar Saudiyya, ya bayyana cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na dawo da martabar da aka rasa a bangaren kiwon lafiya na jihar. A sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, yace Gwamnan ya tuna cewa ba da dadewa ba Likitocin Saudiyya suna Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, domin kula da marasa la...