Fiye da kashi 48 na al'ummar Afrika ba sa samun kulawar lafiya- WHO
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce ‘yan Afrika miliyan 672 wanda ke wakiltar kashi 48 na al’ummar nahiyar basa samun kulawar lafiyar da ya kamata yayinda suke rayuwa cikin cutuka. WHO ta ce dai dai lokacin da kasashe ke baje hajar gagarumin ci gaban da suka samu a bangaren kiwon lafiya, yayin bikin ranar Lafiya ta Duniya har yanzu Afrika na ganin mummunan koma baya a bangaren. Daraktar hukumar WHO shiyyar Afrika Dr Matshidiso Moeti ta ce bangaren kiwon lafiya na ci gaba da samun koma baya a nahiyar wanda ke da nasaba da rashin kulawar shugabanni don habaka sashen. A sanarwar da ta fitar a ranar lafiya ta Duniya wato World Health Day da ke gudana a kowacce ranar 7 ga watan Aprilu, shugabar ta WHO reshen Afrika, ta ce gazawar bangaren lafiya ya haddasa karuwar cutuka a sassan nahiyar da kuma tsanantar cutuka masu hadari. Dr Matshidiso Moeti ta ce abin takaici yadda hatta kananun cutukan da basu kai su yi kisa ba, su ke iya kashe tarin jama’a a nahiyar ta Afrika saboda gurguncewar b...