A Watan Maris Za A Fara Hako Man Fetur A Jihar Nasarawa – NNPC

Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) ya ce a watan Maris Mai zuwa zai fara aikin hako danyen man fetur a karo na farko a Jihar Nasarawa.

Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya bayyana hakan ranar Juma’a, lokacin da ya karbi Gwamnan Jihar, Injiniya Abdullahi Sule da kuma wata tawaga daga Jihar a ofishinsa.

Gano man a rijiyar Keana ta Yamma da ke Jihar ta Nasarawa na zuwa ne kasa da wata biyar bayan kamfanin ya fara hakar wani a rijiyar Kolmani da ke tsakanin Jihohin Bauchi da Gombe.


A cikin sabuwar sanarwar da ya fitar ranar Juma’a, NNPC ya ce, “A ci gaba da aikinsa na gano man fetur a yankunan tsandauri na Najeriya, kamfanin zai fara aikin hako mai a rijiya ta farko a Jihar Nasarawa a watan Maris na 2023.”


Jaridar Aminiya ta ruwaito} Mele Kyari ya ce sakamakon binciken da suka gudanar ya tabbatar da akwai man fetur din dankare a yankin.

Daga nan sai ya bukaci a gaggauta fara aikin saboda ya ce sannu a hankali duniya ta fara dawowa daga rakiyar man fetur zuwa makamashin da ba ya lalata muhalli.

“Dole a gaggauta fara aikin nan saboda komai yanzu na sauyawa a duniya. Nan da shekara 10 ba lallai ne kowa ya yarda ya zuba jarinsa a harkar man ba matukar ba ya san zai ci riba ba. Saboda haka idan muka fara da wuri, ina ganin zai fi,” in ji Mele Kyari.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki