Posts

Showing posts with the label Saurayi

Hisbah Ta Wanke Matar Da Ta Auri Saurayin ’Yarta A Kano Daga Zargi

Image
  Kwamitin da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kafa kan binciken auren matar da ta auri saurayin ’yarta, ya wanke ta daga zarge-zargen da ake mata. Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Alhaji Lawan Ibrahim ya fitar a Kano a ranar Talata. Sanarwar ta ce “Gabatar da rahoton binciken da kwamiti ya ya yi karkashin jagorancin Kwamanda Malam Hussain Ahmed, an gano auren halal ta yi kuma ta cika duk wasu sharuda da addini ya tanadar.” Sanarwar ta kuma ce bincikensu ya nuna cewar matar mijinta ya sake ta tun da fari kuma ta yi iddar wata uku kamar yadda addinin Musulunci ya tsara, kafin daga bisani ta auri saurayin ’yarta da ta daina so. Mataimakin Kwamandan ya yi watsi da zargin da ake wa matar na cewar ita ta kashe aurenta don ta auri saurayin ’yarta. “Auren halal suka yi kamar yadda Musulunci ya tsara, shi ya sa Kwamandan Hisbah a Karamar Hukumar Rano ya jagoranci daurin auren.” Babban Kwamandan Hukumar Hisbah na Jihar, Harun Ibn-Sina, ya jinjina wa kwamitin kan yadda suka gu...