Shirin Karo Karatu A Kasashen Waje: Kason Farko Na Daliban Kano Zasu Tafi Nan Da Watan Satumba- Gwamna Abba K Yusuf
A yayin da ake kokarin ganin an aiwatar da manufar gwamnatin jihar Kano ta shirin bayar da tallafin karatu na digiri na farko a kasashen waje, ana sa ran kashi na farko na daliban da za su ci gajiyar shirin za su bar kasar nan da watan Satumba na wannan shekara. Gwamnan jihar Kano, Alh Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka a fadar gwamnati a ranar Asabar a lokacin da ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Bichi Alh Nasiru Ado Bayero da ‘yan majalisar Masarautar da suka kai gaisuwar Sallah ga Gwamnan. Alh Abba Kabir Yusuf ya kara jaddada kudirin gwamnatin sa bisa fifikon da ake bukata a bangaren ilimi domin gwamnati na shirin sake bude cibiyoyi 20 da gwamnatin da ta shude ta rufe, da makarantun Islamiyya da kwalejojin fasaha a lungu da sako na jihar. jihar da ra'ayin samar da ingantaccen ilimi ga matasa a jihar. Gwamnan ya godewa Sarkin yayin da ya yaba da rawar da sarakunan gargajiya ke takawa a matsayin masu kula da al’adu da yada zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba.