Posts

Showing posts with the label 'Yan canii

CBN Ya Soke Lasisin ’Yan Canji 4,173 A Faɗin Nijeriya

Image
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin gudanar da ayyuka na wasu ’yan canji 4,173 a faɗin ƙasar nan take. CBN ya ce daga cikin ’yan canjin da soke lasisin ya shafa akwai waɗanda suka gaza sabunta lasisinsu, da waɗanda suka gaza biyan wasu caje-caje kuɗin gudanarwa da Babban Bankin ya rataya a wuyansu. Haka kuma, daga cikin waɗanda abin ya shafa akwai masu bijire wa dokokin Babban Bankin kan tsare-tsarensa na yaƙi da safarar kuɗaɗen haram, dakile fitar da kuɗaɗen da ke ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci, da kuma dakile ka’idojin samar da kuɗaɗe. Kazalika, CBN ya ce waɗanda aka soke wa lasisin akwai masu rashin mika wa CBN ɗin bayanan yadda suke sayar da dalar duk mako. Wannan matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da CBN da Gwamnatin Tarayya ke yi na maido da ƙwarin gwiwa a kasuwar canji da musayar kuɗaɗen waje da kuma farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar. CBN dai ya yi alƙawarin ci gaba da bayar da dala ga masu kamfanin canjin kuɗin a kowanne mako kamar yadda aka saba...