Posts

Showing posts with the label Bankuna

Biyan Kudin Haji: Hukumar Alhazai Ta Bauchi Ta Nemi Goyon Bayan Bankuna Kan Fadakar Da Da Alhazai

Image
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi a ci gaba da kokarinta na wayar da kan al’umma kan kalubalen gudanar da aikin Hajji na shekarar 2024, musamman tsadar kudin ajiya da kuma karancin lokacin gudanar da aikin, a yau Alhamis 19 ga watan Oktoba, 2023 ta nemi hadin kan hukumar. Bankunan haÉ—in gwiwa don tallafawa Hukumar a matsayin wani É“angare na Haƙƙin Jama'a na Ƙungiya. Sakataren zartarwa na hukumar Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ne ya yi wannan roko yayin wata tattaunawa da shugabannin reshen bankunan da suka hada gwiwa da hukumar wanda ya gudana a dakin taro na hukumar. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Muhammad Sani Yunusa ya sanyawa hannu, ya ce wannan roko ya zama dole saboda takaitaccen wa’adin da aka ware na aikawa da kashi 50% na ma’aikatun da aka ware wa jihar Bauchi da kuma bukatar maniyyatan da ke da niyyar ilmantar da su da fadakarwa. Ya kara da cewa hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta sake yin kira ga maniyyata da su gaggauta biyan...

Duk wanda ya kwarmata masu É“oye sabbin kuÉ—aÉ—e zai samu tukuici – EFCC

Image
Hukumar yaÆ™i da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce bankunan kasuwanci ne suka janyo tarnaÆ™i wajen ganin sabbin kuÉ—i sun wadata a hannun jama'a. EFCC ta ce bayanai daga Babban Bankin Najeriya sun nuna cewa zuwa yanzu, CBN ya buga sabbin takardun kuÉ—i sama da naira biliyan 400, amma bankuna sun Æ™i fitarwa su bai wa jama'ar Æ™asar. Shugaban hukumar EFCC, Abdurrasheed Bawa a wata tattaunawa da BBC, ya buÆ™aci 'yan Najeriya su tona asirin masu É“oye sabbin kuÉ—i, don ganin hukumar ta je ta Æ™wace su. Abdurrashe Bawa ya ce wannan ita ce mataki na gaba da suke ganin zai taimaka wajen kawo wa talakan Najeriya waraka. Sannan ya tunasar da cewa akwai tukuici mai gwabi ga duk mutumin da ya taimaka aka gano wurare ko mutumin da ke rike da sabbin kudade. 'Ma’aikatan banki ne matsalar mu’ Shugaban na EFCC ya ce babu shaka sun yi na'am da wannan sauyi kuÉ—i, saboda bayanan sirri ya nuna musu cewa akwai mutane da dama da suka boye kuÉ—aÉ—e, suna cinikayya a boye. Sai...

Gwamnoni Sun Roki Buhari A Ci Gaba Da Amfani Da Tsoffin Kudi

Image
  Gwamnonin Jam’iyyar APC sun bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa baki a ci gaba da amfani da tsofaffi da kuma sabbin takardun kudi. Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ne ya bayyana hakan bayan ganawar sirri da suka yi da shugaban kasa a Abuja. Ya ce yayin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya karbi sama da Naira tiriliyan biyu na tsofaffin kudi, amma iya Naira biliyan 300 kacal ya iya bugawa wanda a cewarsa hakan ba zai wadatar da mutane ba. El-Rufai, wanda ya samu rakiyar takwaransa na Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce kamata ya yi CBN ya buga akalla rabin abin da suka tara. Ya ce gwamnonin jam’iyyar sun shaida wa shugaban kasa wawahalar da talakawa ke sha, da asar kayayyaki da ’yan kasuwa ke yi saboda rashin samun masu sayen kayansu. Ya ba da misali da yadda masu sayar da tumatur suka je Legas da kayansu amma suka lalace saboda mutane ba su da kudin saye. El-Rufai ya ce gwamnonin sun roki shugaban kasa da ya sake duba halin da ake ciki. Ya kara da cewar shugaban ...

Daga yanzu Bankuna Zasu Rinka Bayar da Sababbin Kudi A Kan Kanta

Image
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce daga yanzu Bankuna Zasu rinka bawa mutane kudi a kan Kanta, sabanin umarnin da ya bayar na baya kan cewa sai a Na'urar ATM kadai zasu sanya kudaden domin masu hulda dasu su cira. Hadimin Shugaban kan harkokin kafafen yada labarai na yanar Gizo, Bashir Ahmed ne ya wallafa wannan labari a shafinsa na Instagram  Za a iya tunawa cewa A ranar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya Ya gana da Shugaba Buhari ne ya fitar da sabuwar sanarwar da ta ce ko bayan Karewar Wa'adin kashe tsofaffin kudi, Bankuna Zasu ci gaba da karbarsu domin mikawa Babban Bankin 

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Image
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya ce Bankuna za su ci gaba da karbar tsoffin takardun kudi na Naira ko da bayan wa’adin musaya da sabbin takardun kudin da aka zayyana. Idan dai za a iya tunawa, a kwanakin baya ne babban bankin ya kara wa’adin canza shekar kudi naira 1,000 da naira 500 da kuma N200, biyo bayan korafin ‘yan Najeriya. Sai dai a yayin da shugaban na CBN ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan sabon tsarin sauya fasalin Naira da kuma canjin naira a ranar Talata, shugaban na CBN ya ce har yanzu bankuna za su karbi tsoffin takardun bayan wa’adin. Emefiele ya ce idan aka yi la’akari da sashe na 20, karamin sashe na 3 na dokar CBN ta shekarar 2007, ko da tsofaffin kudaden sun rasa matsayinsu na neman kudi, CBN za ta ci gaba da karbar tsofaffin takardun kudi. Mista Emefiele ya ce dole ne bankunan kasuwanci su karbi kudin ko da bayan wa'adin 10 ga watan Fabrairu (SOLACEBASE) 

CBN Ya Zargi Bankuna Da Boye Sabbin Takardun Kudade

Image
B abban Bankin Najeriya (CBN) ya zargi wasu bankuna da yi masa zangon kasa ta hanyar boye sabbin takardun kudade tare da ci gaba da bayar da tsofaffi. Hakan na zuwa ne yayin da ya rage kwana 10 a daina amfani da tsofaffin kudaden kwata-kwata a kasar nan. Babban Jami’in bankin a Jihar Ribas, Maxwell Okafor, ne ya yi zargin a Fatakwal, babban birnin Jihar lokacin da ya jagoranci ayarin CBN yayin ziyarar duba yadda bankuna da kasuwannin Jihar ke ta’ammali da sabbin kudaden ranar Juma’a. Ya ce tsakanin ranakun Alhamis da Juma’a kawai, CBN ya ba bankunan kasuwancin da ke jihar tsabar kudin da suka kai Naira biliyan hudu da rabi, inda ya nuna damuwa kan yadda har yanzu jama’a ba sa samun su. Ya ce, “Mun jima muna sanya idanu a kan yadda ake ba da sababbin kudade, kuma abin da muka gano ba ya karfafa mana gwiwa. “Mun ziyarci wasu bankuna, kuma daya daga cikinsu har yanzu yana bayar da tsofaffin kudi. Wasu injinan ATM dinsu kuma ba sa aiki, kuma mun ji cewar ko kafin mu karaso nan, CBN ya ba s...